AKTH Ya Yi Aikin Fiɗar Ƙwaƙwalwa A Karo Na Biyu

232

Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, AKTH, ya yi aikin Fiɗar Ƙwaƙwalwa, a karo na biyu ta hanyar amfani da na’urar hangen cikin jikin mutum, aikin da ake kira da ‘Pituitary Tumour Surgery’ a likitance.

Majiyarmu ta ruwaito cewa an yi fiɗar ne don a cire wata cuta daga wata mara lafiya, ‘yar shekara 47, Nafisa Yusuf, ‘yar asalin jihar Edo.

Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas, LUTH ne ya turo Misis Nafisa AKTH don yi mata aikin.

Tawagar ƙwararrun likitoci ce ta yi wannan aiki da ya ɗauki tsawon sa’o’i biyar, waɗanda suka haɗa da masu yin allurar kashe zafi, jami’an kula da mara lafiya da likitocin fiɗar ƙwaƙwalwa.

Dakta Musbahu Haruna Ahmed, wani Ƙwararren Likitan Ƙwaƙwalwa wanda ya jagoranci tawagar ya ce Ƙwararrun Likitocin Kunne, Hanci da Maƙogaro, ENT ne suka shige gaba a aikin.

Ya ce likitocin na ENT sun yi nasara wajen shiga jijiyoyin hancin mara lafiyar, kuma suka buɗe hanyar dake zuwa wani ƙashi mai suna ‘sphenoid bone’.

“Likitocin fiɗar ƙwaƙwalwar suka karɓi aiki suka shiga ta ‘sphenoid bone’, suka buɗe tushen ƙwaƙwalwar suka cire cutar.

Dakta Ahmed ya ƙara da cewa an yi fiɗar ne ta hanyar amfani da na’urar hangen cikin jikin mutum da na’urorin ɗaukar hoto na musamman waɗanda suka yi kama da na’urar girma abubuwa da kuma haske mai ƙarfi wanda ya ɗauke su kai tsaye da wasu ‘yan kayayyaki wajen cire cutar ta hancin.

Ya ce tuni an sallami Misis Nafisa daga asibitin bayan ta yi kwana shida a kwance sakamakon aikin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan