Sallamar Hadimai: Osinbajo Na Ƙoƙarin Kamun Ƙafa Da Buhari

254

Tuni Fadar Shugaban Ƙasa ta janye alamomin izinin shiga Fadar Gwamnati daga hadimai 35 da aka sallama na Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, yayinda aka miƙa takardun sallama daga aiki waɗanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, Boss Mustapha ya sanya wa hannu zuwa ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasar.

Labarai24 ta kawo rahoton yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami hadimai 35 daga aiki daga cikin hadimai 80 na Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Majiyoyin cikin gida sun ce an umarci SGF, wanda dama shi ya sanya hannu a kan takardun ɗaukar hadiman aiki da ya miƙa takardun sallama ga hadiman da aka kora.

Da yake tabbatar da miƙa takardun sallamar, wata majiya ta faɗa wa jaridar DAILY NIGERIAN cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa ya yanke shawarar riƙe takardun sallamar har zuwa lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari zai dawo domin kamun ƙafa.

A wani taron tattaunawa na gaggawa da Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Shugaban Ƙasa, Ade Ipaye ya kira, ya yi wa hadiman da sallamar ta shafa bayanin matsayin Shugaban Ƙasa bisa yunƙurinsa na jawo hankalin Shugaban Ƙasar ya janye matakin sallamar.

Ana sa ran Shugaban Ƙasar zai dawo Najeriya ranar 17 ga Nuwamba.

Ƙarfin Mataimakin Shugaban Ƙasa a tsarin tafiyar da mulki yana raguwa a hankali tun lokacin da aka sauya wa wasu hukumomi da yake kula da su zuwa ko dai Ofishin Shugaban Ƙasa ko wasu ma’aikatu.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 16 ga Satumba, Shugaba Buhari ya maye gurbin Majalisar Tattalin Arziƙi da Mista Osinbajo ke kula da ita da Majalisar Bada Shawarar Kan Tattalin Arziƙi wadda za ta yi aiki kai tsaye da Ofishin Shugaban Ƙasa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan