Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar da sallamar hadimai 35 na Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi.
A ranar Laraba, Labarai24 ta kawo rahoton sallamar hadimai 35 daga cikin 80 na Mista Osinbajo da Shugaban Ƙasa ya yi.
A wata sanarwa da Garba Shehu, Mataimakin Shugaban Ƙasa na Musamman Kan Kafafen Watsa Labarai ya fitar ranar Juma’a, ya ce an ɗauki matakin ne don sauƙaƙa yanke hukunci, a rage yawan hukumomi, kuma a rage kuɗaɗen gudanar da gwamnati.
Sanarwar ta ce: “Fadar Shugaban Ƙasa na son tabbatar da cewa a halin yanzu, akwai kwaskwarima da aka yi wa mazaunin gwamnatin ƙasar nan wanda ba a taɓa yin irinsa ba a baya, wanda ya haifar aka sallami wasu masu muƙaman siyasa da dama ko kuma ba a sabunta muƙaman nasu su ba a Wa’adin Mulki na Biyu.
“Wannan kwaskwarima, wadda Shugaban Ƙasa ya bada umarni, an yi ne don a sauƙaƙa yanke hukunci, a rage yawan hukumomi, kuma a rage yawan kuɗaɗen gudanar da gwamnati.
“Kuma amsa ce mai kyau da aka bayar ga tunanin da ake da shi cewa Fadar Shugaban Ƙasa tana da yawan ma’aikata da suka wuce kima, wanda ke kawo matsala wajen ingancin aiki.
“Kamar yadda wata kila al’umma ma’abota hankali za su lura, wasu daga cikin masu muƙaman siyasa da suka yi aiki a ofishin Shugaban Ƙasa ba a dawo da su a Wa’adin Mulki na Biyu ba.
“Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Mai Girma Yemi Osinbajo, bisa bin umarnin Shugaban Ƙasa, an rage masa da yawan waɗannan masu muƙaman siyasa.
“A wajen aiwatar da wannan kwaskwarima, babbar manufar ita ce a alkinta kuɗaɗen masu biyan haraji, a kuma yi wa al’umma aikin da suke buƙata.
“A iya sanin Shugaban Ƙasa, ba wani uzuri da gwamnati za bayar na ƙin yin aiki bayan samun gagarumin goyon bayan mutane na mulkar ƙasar nan tsawo ƙarin shekaru huɗu.
Mai magana da yawun Shugaban Ƙasar, ya musanta cewa akwai tsamin dangantaka tsakanin Shugaban Ƙasa da Mataiamkinsa, yana mai cewa har yanzu dangantaka tsakanin shugabannin biyu tana da kyau kuma da amana.
“Saboda wannan ne, Fadar Shugaban Ƙasa ke son musanta jita-jitar cewa da akwai tsamin dangantaka tsakanin Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari da Mataiamkin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo.
“Dangantaka tsakanin shugabannin biyu tana nan da kyanta, kuma da amana. A tare, za su tsara wa ƙasar nan gaba mai kyau.
“Rahotannin kafafen watsa labarai masu cewa akwai tsamin dangantaka na zuwa ne daga ƙwaƙwale da bakunan masu mummunan fata, waɗanda ke da gurin samo labarai daga Aso Rock Villa don su daɗada wa al’umma.
“Wannan ɓoyayyiyar manufa ita ce dalilin bada fassara ta kuskure ga kwaskwarimar da Fadar Shugaban Ƙasa ta yi kwanan nan.
“An daɗe ana rage ma’aikata. Koyaushe, ma’aikatan Mataimakin Shugaban Ƙasa sun fi na Shugaban Ƙasa yawa, kuma an ta yin tsare-tsare na ganin an rage yawan ma’aikata a Villa.
“Ba an rage ma’aikatan ba ne don a ci zarafin a ƙashin kai ko a raina ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa kamar yadda waɗanda ake ce wa majiyoyin cikin gida da kafafen watsa labarai suka jiyo su suna cewa haka ke nufi.
“Shugaban Ƙasa yana da cikakken iko da gwamnatinsa. Ya kamata kafafen watsa labarai su daina ba wasu mutane iko da kwata-kwata babu shi. Ba wani da ya isa Shugaba Buhari ya kasa juya shi”, in ji Mista Shehu.