Guardiola Zai Jagoranci Wasa na 601 Agobe Lahadi

213

Agobe Lahadi mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City wato Pep Guardiola zai jagoranci wasa na 601 awasan da Manchester City zata fafata da Liverpool.

Za a fafata wannan wasa a filin wasa na Anfield da yamma kuma wasan shine tautaron wasa.

Ga wasannin da Guardiola ya Jagoranta a kungiyoyin kwallon kafa daban-daban daya horas:

A Barcelona ya jagoranci wasanni 247.

A Bayern Munich ya jagoranci wasanni 161.

A Manchester City ya jagoranci wasanni 192.

Ayanzu haka dai Guardiola ya lashe kashi 75 na wasannin daya jagoranta tare da nasarori masu tarin yawa na lashe kofuna.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan