Kamata Ya Yi A Ɗaure Iyayen Yaran Da Aka Sace ‘Ya’yansu A Kano- Sarki Sanusi

546

A ranar Asabar ne Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya yi kira da a tura iyayen yaran nan na Kano da aka yi garkuwa da su, bisa abinda ya kira ‘barin yaransu suna gararamba a titi’.

A ranar 12 ga Oktoba, Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta sanar da cewa ta ceto yara tara da aka yi garkuwa da su daga Kano, aka siyar da su a Onisha, jihar Anambara.

Garkuwa da yaran ya jawo cece-ku-ce da a tsakanin al’umma, inda Jama’atu Nasrul Islam, Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasa, CAN, ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adam da sauransu suka yi Allah-wadai da al’amarin, gwamnatin jihar Kano kuma ta kafa Kwamitin Bincike don bincikar lamarin.

Da yake jawabi a yayin taron yaƙi da shan muggan ƙwayoyi da wata ƙungiya mai suna ‘League for Societal Protection Against Drug Abuse’, LESPADA ta shirya, Sarkin ya ce kamata jami’an ‘yan sanda su tuhumi iyayen da’ laifin sakaci’.

“Game da batun yaran Kano da aka yi garkuwa da su, ina kan tattaunawa da Sarkin Onisha a kan batun. Muna nan muna bin batun.

“Mun ji maganganu marasa daɗi a kan ‘yan ƙabilar Ibo cewa sun sace yaranmu. Shin Ibo gidajenku suka je suka sace yaran? Ko kuma ku ne ku ka bar yaran suna gararamba a titi? Ya kamata mu faɗa wa kanmu gaskiya. Lokacin da iyayen farko suka kawo min rahoton ɓatan ‘ya’yansu, na ce da ina da iko, da na tura iyayen gidan yari.

“Na ma bada umarnin cewa a tambyi Kwamishinan ‘Yan Sanda ko muna da wata doka da ake kira laifin sakaci. Ba mu da wannan doka ne? Duk wanda ya zo ya kawo rahoton sace ɗansa ɗan shekara huɗu a lokacin da yake wasa ya kamata a ɗaure shi. Laifin sakaci.

“Dole Bahaushe ya canza tunaninsa. Koyaushe mukan zargi Ibo, Yarbawa, bayan da a zahiri laifinmu ne.

“A yanzu, ka yi yunƙurin sace yaro a Onisha ka gani idan za ka samu. Ba gaskiya ba ne? Suna barin ‘ya’yansu ‘yan shekara huɗu zuwa uku suna gararamba suna bara?

“Idan ba za ka iya ciyar da iyalinka ba, kada ka tura ɗanka ya je ya yi maka bara. Idan muka ci gaba da rayuwa ta hana ‘ya’yanmu haƙƙinsu, za mu yi kuka, muna zargin wasu.

“Ba ina cewa wasu ba su yi laifi ba ne, na san gobe mutane za su fara cewa ina zargin iyaye bisa garkuwa da ‘ya’yansu. Na san koyaushe ana juya maganganuna. Ban ce ba su yi laifi ba, amma Bahaushe kansa yana da wata karin magana dake cewa: “Idan ɓera nada sata, daddawa ma nada wari”, in ji Sarkin.

Basaraken ya ce al’ummar Hausawa suna nuna sakaci ga iyalansu, yana mai cewa labarin yara da ake samu sun faɗa rijiya yana da dangantaka da rashin nuna soyayya ga iyalai.

“Mutum zai auri mace ba tare da nuna mata soyayya ba. Mutum zai haifi ɗa ko ‘ya ba tare da nuna musu soyayya ba.

“Wannan shi yasa Bahaushe ne kaɗai ke yin watsi da ɗansa. Kamar yadda nake faɗa koyaushe, fadawa za su iya yi min shaida, akwai ƙorafe-ƙorafen da aka kawo mana cewa yaro ɗan shekara uku ko huɗu ya faɗa rijiya.

“Ka bar yaro ɗan shekara uku zuwa huɗu a gida da rijiya a buɗe ka tafi masallaci…….a fahimtata, ka kashe ɗanka. Amma sai ka fara kuka, sai kuma mutane su riƙa tausaya maka. Idan da gaske kana son yaran, me yasa za ka bar shi ya yi wasa kusa da rijiya?

“Ya aka yi yaron ya faɗa rijiya? (Za ka yi ta jin tatsuniyoyi). Babansa ya tafi gona, matar ta fita. Ka bar rijiya a buɗe bayan kana da yaro ɗan shekara uku zuwa huɗu ka bar shi ya yi wasa kusa da rijiya. Duk ƙasar nan idan ba Bahaushe ba ba wanda zai yi haka”, Sarkin ya ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan