Satar Yara A Kano: Ra’ayin Sarki Sanusi Ya Saba Da Ra’ayin Dattawan Jihar Kano

51

A ranar 14 ga watan Oktoba ne rundunar yan sanda a jihar Kano tayi holen wasu mutane da su ka sace kananan yara ‘’yan asalin jihar Kano zuwa jihar Anambra tare da sayar da su a garin Onitsha.

Rahotanni sun nuna cewa ba’a nan kawai ta tsaya ba, bayan satar yaran an canja musu addini daga na musulunci zuwa kiristanci, tare da mayar da su bayi

A bayyana ya ke mafi zaluncin abinda ɗan adam zai yi wa ɗan adam, shi ne abinda yake faruwa akanmu Hausa/Fulani a ƙasar nan.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama a jihar Kano sun lashi takobin bin kadin wannan batu na zargin satar yara daga jihar Kano da yadda ake sauya musu addini, yi musu fyade da kuma canza musu sunaye tare da sayar da su ga ma’auratan da ke bukatar ‘ya’ya.

Manyan kungiyoyin kare dan Adam a jihar Kano sun dauki alwashin tabbatar da an share wa iyayen yaran hawaye, ta hanyar zaburar da gwamnati ta kara kaimi wajen ganin an ceto yaran nasu.

Wannan ya sanya gwamna jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bai wa ma’aikatar shari’a umarni da ta yi wa dokokin jihar Kano kwaskwarima domin zartar da hukuncin kisa ga masu satar jama’a.

Kiran na gwamna Ganduje yana zuwa ne bayan da mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kiran da a kori wadannan miyagun mutane da su ke satar yayan al’ummar jihar Kano daga garin Kano, a daya bangaren kuma wata kungiyar dattawa masu kishin jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Bashir Othman Tofa ta koka kan satar yara da ake yi a jihar ana kai su kudancin kasar.

Kungiyar ta bayyana ra’ayinta kan wannan batu ne ta bakin mataimakin shugaban kwamitin yada labarai na kungiyar Mallam Ibrahim Ado Kurawa.

Ado Kurawa ya ce akwai bukatar gwamnatin jihar Kano ta hada kai da ta jihar Anambra domin nemo sauran yaran da su ma iyayensu ke kukan bacewarsu lokaci mai tsayi ba a gansu ba har yanzu.

A daya bangaren kuma matasa yan takarda sun yi Allah wadai da faruwar lamarin, musamman a kafafen yada labarai na zamani, tare da bukatar a yiwa wadannan yara adalci.

Amma a jiya sai ga wasu kalaman bazata sun fito daga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II yana furucin a garkame iyayen da aka sacewa yaya a kurkuku, sakamakon sakacin su na barin su suna gararamba a tituna ba bisa cikakkiyar kulawa ba.

Wayyo Allah talaka bawan Allah! Ina laifin a ce Sarki Sanusi II Allah wadai ya yi da wannan mummnar dabiar da yan kabilar Ibo su ke yiwa Hausawan da su ka ba su masauki a cikin unguwanninsu.

Kowa ya sani bahaushe yana da sakaci akan komai na rayuwa, amma babu wani mutum da za’a ce wai yana sane ko kuma tsabar sakaci ya bari an sace masa dan da ya haifa a cikinsa.

Babu shakka al’ummar jihar Kano sun yi matukar kaduwa tare da juyayin irin wannan furuci daga bakin Sarki Sanusi II.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan