Tauraron Wasa Ayau Katsina United da Enyimba

173

Ayau za a buga wasannin mako na biyu na gasar ajin Premier ta kasar nan tsakanin kungiyoyin kwallon kafa daban daban afadin tarayyar kasar nan.

Saidai daga ciki akwai tauraron wasa wanda shine wasa mafi zafi acikin wasannin, wasan kuwa shine tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Katsina United da Enyimba.

Amakon farko dai Enyimba basu buga wasaba sakamakon sun tafi kssar Afrika ta Kudu domin buga wasan zagaye na biyu da TS Galaxy agasar ajin kwararru ta nahiyar Afrika inda sukayi nasara.

Itakuwa Katsina United tayi rashin nasara awasan farko na gasar ahannun Abia Warriors.

Saidai tuni dan wasan tsakiya na Katsina United ya bayyana cewar sufa yau maki 3 sukazo samu akan Enyimba.

Shima shugaban kungiyar kwallon kafan ta Katsina United wato Prince Abdussamad Badamasi ya bayyanawa kafar yada labarai ta Labarai24 da Wasa.ng cewa insha Allah zasu sami nasara akan Enyimba.

Inda ya kara da cewar “Enyimba suna da ‘yan wasa kuma haka muma muna da ‘yan wasa gogaggu saboda haka idan Allah ya yarda zasu sami maki 3 akansu tunda tarihi yakan maimaita kansa wajen ganin cewar Enyimba basa iya samun nasara agarin Katsina”

Henry Makinwa shine mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Katsina United inda shima yayi fatan samun nasara awasan na yau.

Haka shima Usman Abdallah mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Enyimba yace burinsu shine susami nasara awasan na yau.

Saidai Makinwa da Usman Abdallah kar tasan karne tunda kowa kwararren mai horas wa ne.

Za a fara wannan wasa da misalin karfe 4:00 na yamma afilin wasa na Katsina United.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan