Jam’iyyar hamayya ta PDP a Kano, ta ce tana zargin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ƙoƙarin sauya alƙalan da za su saurari ƙarar da ta ɗaukaka game da zaɓen gwamnan Kano.
Ɗan takarar PDP, Abba Kabir-Yusuf yana ƙalubalantar hukuncin Kotun Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Zaɓen Gwamna ta Jihar Kano wadda ta bayyana gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaɓen dake cike da cece-ku-ce.
Majiyarmu ta ruwaito cewa a wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 28 ga Oktoba, 2019, mai lamba PCA/EPT/APPEALS/2019/VOL II, Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta kafa gungun alƙalai da za su saurari shari’ar waɗanda Mai Shari’a M.A. Owode zai jagoranta.
Amma a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi da daddare, jam’iyyar hamayyar ta yi zargin cewa akwai wani shirin sauya alƙalan dake kan hanya don sauya alƙiblar shari’ar.
“PDP tana sanar da makirce-makirce da APC da wakilan Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje na sauya Gungun Alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙarar Zaɓen Gwamnan Kano.
“Jam’iyyar kuma na son sanar da makirce-makirce da maye gurbin alƙalai da marasa gaskiya, waɗanda tuni an siye su an yi musu bayani don canza shar’ia su yi abinda APC do Gwamna Ganduje ke so.
“Jam’iyyar PDP tana gayyatar ‘yan Najeriya su lura da cewa zaman gungun alƙalan, wanda aka canza daga Litinin, 11 ga Nuwamba zuwa Talata, 12 ga Nuwamba, 2019 saboda hutu an ɗaga shi har sai illa ma shaa Allahu.
“Muna da rahotanni dake cewa wannan na faruwa ne sakamakon matsin lamba da APC da wakilan Gwamna Ganduje ke yi don sauya sunayen alƙalan.
“An kuma sanar da jam’iyyarmu daga majiya mai tushe cewa an ɗaga zaman kotun ne har sai illa ma shaa Allahu don bada damar maye gurbin alƙalai da aka sanar tuni, waɗanda za su juya tsarin shari’a don ba jam’iyyar APC nasara.
“Tuni, magoya bayan Gwamna Ganduje sun fara murna, suna iƙirarin cewa su sun wuce Kotun Ɗaukaka Ƙara, duk da gungun alƙalan ba su fara zama ba.
“‘Yan Najeriya za su iya tuna abinda ya faru lokacin haɗa sunayen alƙalan Kotun Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Zaɓen Gwamna ta Kano, lokacin da aka sauya alƙalan farko, bayan nan kuma aka yi hukuncin da ya daɗaɗa wa Ganduje da jam’iyyar APC ba tare da lura da buƙatun jama’a ba.
“Da wannan makircin da jam’iyyar APC ke ci gaba da yi, magoya bayan Ganduje sun fara bugar ƙirji cewa alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙarar, waɗanda tuni an sanar da sunayensu, kuma ake sa ran su fara zama ranar Talata, za a tilasta musu su biya buƙatar jam’iyyar APC da Gwamna Ganduje.
“Jam’iyyar PDP na gargaɗin cewa duk wani sauyi a jerin sunayen da tuni aka kafa zai iya kawo tashin-tashina da rikici a jihar, duba da yadda mutane ke so a yi adalci.
“Saboda haka, jam’iyyarmu na kira ga Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara, Zainab Bulkachuwa, da kar ta bari wani ya jefa ta cikin wannan da’ira ta hanyar tabbatar da cewa ba a sauya alƙalan da aka kafa ba tuni.
“‘Yan Najeriya, musamman al’ummar Kano suna kallon”, in ji sanarwar.