Bawon ayaba na kunshe da sinadarai masu dumbin yawa wadda ke da mutukar amfani ga lafiyar jiki. Bawon ayabar na kunshe da sunadarai kamar haka:
Patassium, zinc, amino, da vitamin Wanda zasu jiki ya samu lafiya cikin jiki. Kana bawon ayabar na taimako wajen gyran jiki da tsatso da kyau domin yana dauke sinadarin:
carbohydrate, vitamin, B6, B16, antioxidant, mineral hade da magnesium wadanda ke raya kwayoyin halitar jiki, maganin cizon sauro, kurajen jiki gami da sanya hasken hakori.
Bincike masana kimiyar sinadaran ‘ya’yan itatuwa da aka gabatar a shekara ta 2011 da 2018 yayi nuni zuwa ga tarin sunadarai da magunguna da bawon na ayaba ke yi.
Duba da irin muhiman sunarai musaman antimicrobial, antioxidant da phenolic, bioactive kamar polyphenol, carotenoids sanan hadi da anti-inflammatory wanda ke sa kunar rai.
Amfanin bawon ayabar wajen warkar da yankwanar fuska
Yadda za a yi domin maganin yankwanar fuska
A hada bawon ayaba da gwaiduwar kwai a cakuda su sosai.
A shafa hadin a fuskar sarai
A bar shi na tsawon dakika 5 (minti)
Sanan sai a wanke fuskar
Za a maimaita hakan sau uku a sati
Domin goge tabo (miki)
Yadda za ayi domin goge tabo
Daka bawon ayabar a shafa a kan tabon
A bar shi na tsawon sa’a guda ko dukkan dare
A maimaita hakan kullum

Domin magance kaikayin fata
A shafa bawon ayaba a daidai yadda yake kaikayin
Abar shi na tsawon dakika 10-15
Sanan a wake
Yadda za ayi domin magance kurajen fuska (pimples)
Shafe illahirin fuskar
A bar shi har tsawon dakika 5-10
Sanan a wanke fuska
Ana shafawa sau biyu a rana.
Domin magance dabbare-dabbaren fata, a kankaro wanan farin na jikin bawon ayabar sai a hada shi alobera (aleo vera) sanan a na shafawa.
Sanan ake shafawa.
Domin samun hasken fata
Sanadaran hadawa
Bawon ayaba guda daya
Cukali 2 na garin alkama
Cukali 2 na sukari
Cukali 1 na danyar madara
Sai a hada
Bayan an kirba bawon ayabar a hada da garin sukarin da na alkama
Sanan a shafa jiki duka sosai
A wanke bayan minti 20-30
Domin sa laushin fata
Yadda ake hadawa
A nuke bawon ayaba sanan a shafe fuska amma a kiyaye kar ya shiga baki ko idanuwa.
A wanke fuska da ruwan sanyi
Domin magance maikon fata
Yadda ake hadawa
Nike bawon nunanar ayaba
Hada shi da zuma cukali 1
Da rabin cikin cukali na lemon
Sai a shafe fuska.
Domin goge hakora suyi haske tas
A gutsiri bawon ayaba, a shafa shi a hakori
A bar shi na tsawon minti 10-15
Sanan a goge shi
A tabbatar da yin amfani da bawo mai kyau kuma kar a ajeyi shi a firji.