Maganar gaskiya, duk lokacin da aka ce shugaba na siyasa ko sarauta yayi kuskure, to kamata yayi a nuna yayi kuskure ta hanyar amfani da lafazi mai kyau da mutuntawa. Ba don komai ba sai don kasancewarsa shugaba. Saboda shi ba ma’asumi bane. Amma abun mamaki, idan aka ce yau wani malami na addini yayi kuskure, a madadin wasu su yi posting cikin mutuntawa da girmamawa da jan hankali, sai ka ga suna yiwa mutuncin malamin nan d’iban karen mahaukaciya. Amma idan basaraken da suke qauna ne ya kwafsa, sai ka ga suna ta yiwa abun kwaskwarima da samawa kuskuren da yayi gindin zama.

Sanin kowa ne batun sace yara guda tara y’an asalin jihar Kano, bayan an siyar da su kuma aka canja musu addini da sunansu na asali. Malamai da wasu daga cikin y’an siyasa sun tofa albarkacin bakinsu. Jama’a da dama Allah Allah suke su ji sautin Sarki Muhammadu Sunusi II akan batun amma shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu. Kwatsam, jiya sai ga sarki na cewa “Shin Inyamuran da suka sace yaran nan har gida suka bisu? Ko kuma iyayen su ne suka watsar da su a titi suke ta gallafiri?” Anan Sarki ya nuna cewa yaran da aka sace kamar almajirai ne da suke yawon bara ko kuma irin yaran da sun damu iyayensu a cikin gida za a koro su waje. A qarshe Sarki ya qara da cewa kamata yayi a kama iyayen yaran a hukunta su. Ikon Allah. Ji wani qarfin hali!
A haqiqanin gaskiya yaran nan ba almajirai bane. Yawancinsu yara ne qanana, wasu ma y’an makarantar Islamiyya ne. Acikin yaran akwai wani Faruk wanda duk ya fi su girma. Da muka samu labarin cewa in ance yayi sallah sai yace shi ba Musulmi ba ne sai da muka je gidansu. Mun tattauna da mahaifiyar yaron ta ce mana wata mata ce mai siyar da masara a kusa da gidansu ta sace yaran. Ka ga maqociyarsu ce kenan. Kuma a unguwar yara guda goma sha d’aya aka sace amma Faruk ne kad’ai ya dawo. Wallahi yaron halittarsa da d’abiunsa duk sun koma na Inyamurai. To haka ma sauran yaran, yawancinsu a unguwanninsu aka sace su. Ba wai sun fita yawon bara ne kamar yadda shi Sarki yake zato ba. Akwai masu cewa su da suna yara duk inda za su ana had’a su da babba a gidansu, to don Allah kana tsammanin yadda al’umarmu take a shekaru talatin ko arba’in da suka wuce haka za ta kasance yanzu? Yawancinmu fa mun karanta yadda al’ummah take canjawa sakamakon wasu sababbin abubuwa da suka zo da tsarin mulki da zamantakewa da sauran abubuwa.
Bugu da qari, yaran nan ko almajirai ne shin daidai ne a sace su a Kiristan da su a mai da su bayi? A qa’idar rayuwa, a duk lokacin da bala’i ya samu mutum jajanta masa ake yi. Idan mutum yana da laifi daga baya sai a fad’a masa. Yanzu misali, idan ka zo ka ga yarinya kwance cikin jini an mata fyad’e, sai ka ga shigar da tayi ta banza ce, yanzu shikenan sai ka hauta da fad’a ka ce laifin ta ne da ta sa matsattsun kaya? Yanzu idan 6arawo ya ma sata a kasuwa, shikenan sai ace laifin ka ne da ba ka adana kud’in ka yadda ya kamata ba? Shin da 6arawon da ya haura gidanka ya ma sata, da wanda ya ma sata a waje, ya sunan abar da ya ma?
Na ga wani d’an kanzagin sarki na cewa ai yaran da aka sace gabad’aya y’ay’an talakawa ne. Babu yaran G.R.A (look at this insensitivity and irresponsibility). To shin za6un mutum ne Allah yayi shi talaka? Idan mai kud’i Allah ya hore masa ya gina qaton gida, ya sa gate, ya warewa yara d’akin wasa a gidansa da su TV game da sauransu, shi kuma talaka da ke gidan haya don ya turo yaransa qofar gida ko dandali su yi wasa shikenan sai ace yayi laifi? Ga duk wanda ya san Sarkinmu ya san ya na adawa da yadda ake yawan haihuwa a garuruwanmu. Kuma yana yaqi da “almajiranci.” Yawancinmu muna bayyana damuwarmu akan hakan a wasu lokutan musamman yaran da ake turo su bara da sunan karatu. To a madadin Sarki ya qyale wannan abun da ke damunshi a yanzu a maida hankali wajen nemo sauran yaran da aka sace mana, sai kawai ya amayar da fushinsa akan al’ummar da yake mulka.
Maganar da Sarki yayi jiya na cewa kamata yayi a ladabtar da iyayen yaran ta samu kar6uwa sosai a kudancin qasarnan. Sai yad’a maganar suke suna jin dad’i suna nunawa duk al’ummarmu babu mai hankali da ilimi da fad’ar gaskiya sai Sarki Sunusi II. Wannan ba qaramin zubar mana da qima ba ne wallahi. A duk lokacin da za a ce Sarki na jin kunyar kasancewa da mutanen da yake mulka to babu wani ci gaba da za a samu ta 6angarensa. Kuma wallahi bai kamata ace ya ci gaba da kasancewa da wannan al’ummar ba tunda haushinta yake ji! Kuma yanzu tsammanin Sarki idan Sallah ta zo iyayen yaran nan za su fito kallonsa suna d’aga hannu suna cewa Allah ya ja zamaninka? Yanzu idan yaran nan suka girma suka yi hankali, sai suka ji labarin abun da Sarki ya ce akan su, don Allah me kuke tsammani za su ce?
Ga wanda ya dad’e yana bibiyar maganganun Sarki Sunusi II, qimanta alaqar da ke tsakaninshi da arnan abokananshi y’an kudancin qasar nan ba wani baqon ba ne. Ya na son su sosai. Ba ya son sa6a musu in ba dole ba. Tun lokacin da abun nan ya faru ake ta qoqarin ceto sauran yaran da hukunta wad’anda suka sace su, mai girma gwamna har hukuncin kisa ya ce za a yankewa duk wanda aka kama da laifin nan, yanzu shi kuma Sarki ya maida hannun agogo baya. A madadin a ci gaba da bincike, yanzu za a d’au tsawon lokacin ana ta sharhi akan maganarsa, qarshe ma binciken da ake duk a watsar. Domin masu garin sun ce laifin iyayenmu ne da suka haifo mu suka sake mu a titi.
A qarshe, wannan maganar ba ta kamata ta fito daga bakin Sarkinmu ba. Kamata yayi ace qazamai irin su Nnamdi Kanu ko FFK ne za su yi mana wannan cin fuskar ba jikan Dabo ba. Zai yi kyau Sarki ya janye maganar da yayi ya d’an yi wata kwaskwarima yace ba a fahimce shi ba. Ya kuma bawa iyayen yara haquri a wuce wajen kawai. Allah ka shiryi Sarkinmu. Ka sa masa kishinmu da qaunar talakawansa. Ka ba mu ikon yi masa biyayya a inda yayi daidai. Ka bamu ikon fad’ar gaskiya akan shi lokacin da yayi kuskure, ameen.