Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, mai kowa mai komai, Wanda ya bani damar yin wannan ‘yar gajeriyar tunatarwa zuwa ga Mai Martaba Sarkin Kano da dukkan daukacin Al’umma masu irin ra’ayinsa game da satar yara da ake tayi a kwaryar birnin jahar Kano.
Wanda sanin kowa ne, Allah ya bawa Mai Martaba sarki baiwar ilimin addini da na zamani. Hakan kuma yana taimaka masa wajan iya gogayya da jama’a a duk fadin duniya. Amma sau da yawa sarki yana fadar gaskiya kuma tana yiwa mutane dadi. Amma a wannan jikon Sarki ya yi maganganu masu ban mamaki da ban al’ajabi, wanda muke ganin sarki ya yi tuntuben harshe ba haka ya kamata yace ba.
Ko shakka babu, abubuwa da dama sun faru da mai martaba sarki na wajan kasa fahimtar irin ra’ayoyin shi. Wanda sau da yawa mu mukanyi uwa da makar diya wajan wayar da kan al’umma. Amma a wannan karo bama tare da sarki. Saboda yaci karo da tsarin mu’amalar rayuwa dama tsarin koyarwa ta addinin musulunci.
Sanin kowa ne Annabi(S.A.W) yana fada a cikin wani sahihin hadisi yana cewe ” Musulmi ya fadawa dan uwansa Musulmi magana me dadi sadaka “CE”. Ni na dauka mai martaba sarki zai fada musu maganganu masu nutsar da zuciya, ba kalaman da za su sa iyayen yara jimami ba.
Mai martaba sarki ya kamata yasan akwai bambanci tsakanin ‘ya’yan talakawa da ‘Ya ‘yan masu kudi. A cikin talakawan ‘yayansu suna zuwa makarantu kama daga na BOKO zuwa na islama. Wanda sau da yawa yaran nan da Kansu suke tattaki zuwa wadan can makarantu sabanin abun yadda yake a gidan masu hannu da shuni.

Ni dinnan zan iya tuno lokacin da muna yara muke zuwa marantar firamare da islamiyya a kafa. Wanda muke tafiyar kimanin kilomita shida (6) zuwa da dawo wa. Amma tun a lokacin ‘yayan masu kudi a mota ake kaisu. Saboda haka babu yadda shugaba zai zargi iyaye da laifin barin yara suna fita daga gida. Ko kadan yin hakan ba dai dai bane.
Maganar da mai martaba Sarki yayi ka iya tsunduma iyayen yara su fada zuwa cutar damuwa da tunanunnuka (wato depression). Wanda ba karamar illa bace a garesu.
Amma ina son mai karatu ya fuskanci zance na ba ina nuna iyayen yara basu da laifi ba. Su ma iyayen yara ya zama dole su kula da ‘yayansu sosai.
Muna kira ga mai martaba sarki da ya yi gaggawar bawa jama’ar jihar Kano hakuri musamman iyayen yaran da suka salwanta.
Allah ya bayyana mana su, Allah ya kiyaye gaba, Ameeen.
Daga: Khalid Sunusi Kani
Ra’ayin da aka bayyana a cikin wannan rubutu na mai rubutun ne kawai, bai zama lallai ya zamto iri ɗaya da na Labarai24 ba.
Za a iya samunsa ta Email: khalidsunusikani13@gmail.com ko 07030631259
[…] Muƙalar Da Ta GabataTirƙashi: Wani Saurayi Ya Yiwa Surkin Kano Nasiha Mai Ratsa Zuciya […]