Ga Masu Aure Kawai: Sirrin Yin Jima’i Ga Lafiyar Ɗan Adam

191

Binciken masana ilmin soyayya ya yi nuni akan yadda kauna, taba jiki hada da yin jima’i ke amfanar mutum wajen rage fargaba, samar da kwanciyar hankali da nishadi gami da walwala da ma aurata ka samu bayan yin jima’ i da safe.

Hakan na nufin za su ji wasai-wasai ba tare da wata damuwa da ke bujirowa sanadiyar kujuba-kujubar yau da kulum ba.

Yin jima’i akalla sau daya a sati zai yi amfani wajen wanzar da lafiyayar kwakwalawa, sanadarin (hormones) da tabbacin bugun zuciya lafiyayye.

Yawanta yin sa kamar sau uku ko fiye a sati na nufin samun isassar lafiya domin shi jima’i na rage yiyuwar kamuwa da ciwon zuciya da 50% ga mazaje. Sanan ga wanzar da samun nishadi da ka dauke damuwa.Amfanin yin jima’i ga lafiyar zuciya
Atisaye na dumbin amfani ga zuciya haka zalika jima’i daidai yake da mosta jiki sama-sama kai harma jima’i din na kara bugun zuciya ya kai kololuwarsa tamkar an motsa jiki yayin fitar ruwan mani domin daga zarar sha’awa ta riski mutum sako zai isa zuwa zuciyarsa yayin da bugun ta zai karo har izuwa karshe ma’amala.

A wanan yanayi masana sun ce zuciya na bugu irin na hawa matattakalar beni.

Amfanin jima’i bai kare a jin dadi kadai ba, domin maza dake jinkirin yinsa kamar sau daya a wata na iya kamuwa da mastalar zuciya fiye da wanda ke yi sau biyu a sati.
Bayan samar da damar yin barci ingantace, jima’i na taimako wajen narkewar abinci a jiki gami da su muhimman amfani da za su a so aikata jima’i akai-akai.

. Jima’i na rage damuwa
Kamar yadda atisaye ke habaka jiki haka shi ma jima’i ke taimako wajen sakin sinadarin (hormenes) da ke bujuro da anushuwa da kara yawan (serotonin) wanda ke taimakawa aikawa kwakwalwa sako kana ya rage damuwa.

. Jima’i na taimako wajen tsawon rayuwa
Duk shekarun mutum jima’i na sa shi farin ciki da zai iya karawa mutum kimanin shekaru 8 a bisa shekarun sa a duniya.

Kwarai ta hanyar morewa tare da iyali a kan iya samun tsawon rayiwa domin a lokacin saduwa a kan narkar da abinci da aka ci, gami da samar da zuciya mai lafiya tamkar kana motsa jiki ga kwanciyar hankali da morewa cikin nishadi tabbas za a habaka garkuwar jiki da Kara tsawon rayuwar mutum.

Yawan biyan bukata yawan tsawon rayuwa da karin samun kariya daga cuta da 20% a maza kana mata na samun kariya daga ciwon zuciya da 30% in suna samun biyan bukata kamar sau biyu a sati.Jma’i na rage yiwuwar kamuwa da ciwon daji
Akwai kebantaccen amfani ga lafiyar maza kamar yadda bincike ya nuna cewar yawan biyan bukatuwa kamar sau 21 ko fiye da haka ka iya rage kamuwa da ciwon daji sabanin karancin biyan bukatuwa.

Duk da cewar dai ciwon daji da ake Kira prostate cancer din na da hanyoyin magance shi da dama, amma yin jima’i ne daya da yake da sauki.
Masanan sunyi nuni da cewa biyan bukatar zai iya kasancewa ta kowace hanya mudin dai an gamsu to hakan yayi.

5 Jima’i na sa kuruciyar mutum ta dade
Ba sai an kai ga yin sojiri (Tiyata) ko shafa man dame fata ba, jima’i na sa a kasance da kuraciya kuma ana sheki tamkar an sabunta mutum.
Domin yawan saduwa na samar da sinadaran estrogen da testrogen da ke tsafto da kuruciya da gyara mutum tas-tas.

Abin mamaki a nan ko shine a wani gwaji alkalan tantance shekarun mutane sun gano cewa wanda ke jima’i kamar sau 4 da mutum guda a sati na da kuruciya kasa 7 zuwa 12 na asalin shekarun su na haihuwa.
Kuyi ta jima’i amma ayi na halak ga daɗi ga kuma lada.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan