An Haramta Karuwanci A Cikin Maiduguri Da Kewaye – Shehun Bama

1316

Mai martaba Shehun Bama Kyari Ibn Umar El-Kanemi, ya bayyana haramta harkokin karuwanci a masarautarsa.

Sakataren Sarkin, Abba Shehu Umar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin a birnin Maiduguri.

Shehun Bama ya koka kwarai da yadda al’amuran karuwanci ke kara bunkasa a yankin Galadima da ke a birnin Maiduguri duk kuwa da kokarin da aka yi na rufe gidajen Magajiya da ke a yankin.

Shehun Bama ya bayyana cewa duk wanda aka kama yana saukar karuwai a gidansa zai gurfana a gaban kuliya, kuma za a rushe gidan kamar yadda dokar jihar ta tanadar.

Shehun Bama ya umarci dagatai da masu unguwani da su sa ido don dakile harkokin karuwanci a jihar musamman ma a wannan lokaci da gwamnati ta tsaurara matakin dakile harkar a Maiduguri, domin hakan na nufin karuwan da masu nemansu da ma masu basu gidaje za su koma wasu kananan hukumomi don ci gaba da harkokinsu.

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan