Barcelona Suna Neman Wanda Zai Maye Gurbin Valverde

264

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona sun shiga neman mai horas war da zai maye gurbin mai horas dasu na yanzu wato Valverde.

Inda sukace mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool wato Joggin Klopp shi suke da sha awar kawowa kungiyar.

Mafi yawa dai masu ruwa da tsaki na Barcelona suna daukan mai horas war dayayaba buga wasa a kungiyar ne, amma yanzu wasu daga cikin mahukuntan kungiyar ta Barcelona sunce babu wanda ya dace ya horas da Barcelona face Joggin Klopp.

Klopp dai shine ya jagoranci Liverpool ta lashe gasar zakarun nahiyar turai a kakar wasa ta bara inda har gada sukayi da Barcelona.

Ayanzu dai Liverpool tanayiwa Joggin Klopp dadi inda yakecin karensa babu babbaka.

Shin ko Joggin Klopp zai iya karbar tayin kungiyar kwallon kafa ta Barcelon?

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan