Fitaccen Mai Adawa Da Ganduje, Dadiyata, Ya Yi Kwana 100 A Hannun ‘Yan Garkuwa

1090

Har yanzu ba a gano shahararren mai adawa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ba, kwana 100 bayan an sace shi daga gidansa dake Kaduna, abinda yasa iyalinsa suka fara fitar da rai.

Abubakar Idris (da aka fi sani da sunan ƙarya: Dadiyata), shahararren mai amfani da shafukan sada zumunta, wanda aka san shi da sukar Gwamna Ganduje da jam’iyya mai mulki, wato APC, wasu mahara ne da har yanzu ba a gane ko su wane ne ba suka sace shi a gidansa ranar 2 ga Agusta.

Mutanen ɗauke da makamai sun shiga gidansa a unguwar Barnawa lokacin da yake dawowa da misalin ƙarfe 1:00 na dare.

Mutanen, waɗanda iyalin Mista Idris suka ce suna sanye da jajayen huluna, sun dira a kansa, suka tafi da shi a cikin motarsa, ƙirar BMW.

Ita ma motar har yanzu ba a gano ta ba, wata uku bayan sace shi.

Ɗan shekara 34, malamin jami’a, an san shi da nesanta kansa da Gwamna Ganduje da manufofisa a Kano, amma yana zaune a Kaduna tare da iyalinsa tsawon shekaru.

Gwamnatin dai ta nesanta kanta da garkuwar da shi.

Koda yake jami’an ‘yan sanda sun ce sun ƙaddamar da aikin ceto Mista Idris daga waɗanda suka yi garkuwa da shi, har yanzu ba a kai ga gano shahararren mai yin sharhin a kafafen sada zumunta na zamani ba kwana 100 bayan garkuwa da shi.

Haka kuma ‘yan sanda sun ce sun samu bayanan sirri da yawa, amma har yanzu ba wani bayani da ya taimaka wajen gano Mista Idris.

‘Yan rajin kare haƙƙin bil Adama da dama sun shiga kiraye-kirayen da ake yi wa hukumomi na tabbatar da cewa Mista Idris ya dawo cikin iyalinsa lafiya lau.

Ƙungiyar Amnesty International ta buga wata ‘yar takarda da hotonsa a matsayin ɓangaren wani kamfe na tilasta gwamnati ta gano shi.

Haneefa Idris, mai ɗakin Mista Idris ta ce kullum fatan iyalin yana gushewa ba tare da samun labarin inda mijinta yake ba.

“A yanzu mun ƙara fusata, amma ba ma so mu yi tunanin abubuwan da ba su kenan ba a yanzu”, mai ɗakin Mista Idris ta shaida wa majiyarmu haka a wata hirar waya ranar Talata da yamma.

“Muna samun jita-jita da yawa game da inda yake, amma ba mu iya tabbatar da ko ɗaya ba”, ta ƙara da haka.

Mai ɗakin Mista Idris ta ce jami’an ‘yan sanda dake aiki a kan batun garkuwar da shi suna tuntuɓar iyalin, kuma sun yi alƙawarin yin iya bakin ƙoƙarinsu.

Mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kaduna, Abubakar Sabo, ya faɗa wa majiyarmu cewa yadda aka yi garkuwa da Mista Idris baƙon abu ne a jihar, jihar da ke da wasu daga cikin rahotannin sace mutane mafiya yawa.

Yawancin masu garkuwa da mutane sukan tuntuɓi iyalin waɗanda suka sace a cikin sa’o’i 24 zuwa 48, amma Mista Sabo ya ce yadda aka sace Dadiyata baƙon abu ne, tunda an shafe makonni ba tare da an tuntuɓi wani ba.

“Abin kaico, wannan bai yi kama da irin garkuwa da mutanen da ake yi da muka sani ba”, a cewar jami’in ɗan sandan, wata ɗaya bayan afkuwar al’amarin. “Ba su kira waya sun ce a biya su kuɗin fansa ba, kuma ba su bayyana a ina yake ba”.

Ba a iya samun Mista Sabo ba don ya yi bayanin matsayin binciken ‘yan sanda game da al’amarin kwana 100 bayan afkuwar al’amarin.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan