Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Soke Zaɓen Gwamnan Oyo

289

A ranar Litinin ne Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zama a Ibadan, babban birnin jihar Oyo ta yi watsi da hukuncin Kotun Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Zaɓen Gwamna ta Jihar Oyo, wadda ta bayyana gwamnan jihar, Seyi Makinde, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

Bayo Adelabu, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, shi ya shigar da ƙarar inda yake ƙalubalantar nasarar da Mista Makinde na jam’iyyar PDP ya samu.

A hukuncin da alƙalai huɗu suka rinjayi alƙali ɗaya, gungun alƙalai biyar na kotun sun ce hukuncin waccan Kotun Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Zaɓen Gwamnan kuskure ne, amma Kotun Ɗaukaka Ƙarar ba ta bada umarnin a gudanar da sabon zaɓe ba ko kuma a ƙara sauraron ƙarar.

Kotun ta tabbatar da cewa an samu kuskure a hukuncin Kotun Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Zaɓen Gwamnan, kuma an keta alfarmar Mista Adelabu ta damar sauraro.

Kotun ta ce ba za ta iya bada umarnin sake sauraron ƙarar ba saboda kwanaki 180 da doka ta tanada Kotun Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Zaɓen Gwamnan ta yanke hukunci sun ƙare.

Majiyarmu ta ce dukkan waɗanda suke cikin ƙarar suna shirin ɗaukaka ƙara a Kotun Ƙoli bisa wannan hukunci mai ɗaure kai.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan