Nigeria Sun Lallasa Zambia Daci 3 da 1

124

Kungiyar kwallon kafa ta ‘yan kasa da shekara 23 ta lallasa kssar Zambia daci 3 da 1.

Dan wasan Zambia Patson Daka ne ya fara jefa kwallo a ragar Najeriya a mintina na 12, daga bisani dan wasan Najeriya Orji Okwonkwo ya rama a mintina na 16.

Bayan andawo daga hutun rabin lokaci ne Kelechi Nwakali yakara jefa kwallo ta biyu a mintina na 65, gaf daza a tashi daga wasan dan wasan Najeriya Awoni ya jefa kwallo ta 3 adaidai mintina na 90.

Yanzu dai Najeriya nada maki 3 daga wasanni 2 data fafata inda tayi rashin nasara awasan farko ahannun kasar Ivory Coast.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan