Wani Suruki Ya Sa An Kama Uban Matarsa Tare Da Alkalin Da Ya Daura Mata Aure.

247

Jami’an tsaron yan sanda da ke yaki da yan fashi da makami sun kama tsohon shugaban kamfanin Fijo na kasa, kuma fitaccen attajiri a garin Kaduna, Alhaji Sani Dauda akan rikicin da ya biyo bayan aurar da yarsa da ya yi.

Tun da farko wasu rahotanni sun bayyana cewa surukin Alhaji Sani Dauda, kuma tsohon mijin ‘yar ta sa Naseeba ne ya umarci yan sanda da su kama Alhaji Sani Dauda, tare da dansa Shehu Dauda da kuma alkalin kotun Musulunci dake Magajin gari, Murtala Nasir, wanda shi ne ya daura auren Naseeba da wani sabon miji.

Wata majiya ta bayyana cewa an daura auren Naseeba da wani mijin ne a ranar Asabar din da ta gabatar, wanda hakan ya yi matukar batawa tsohon mijinta na ta rai. Bisa wannan dalilin ne ya sa jami’an yans anda suka kama masa tsohon sirikin na sa da sauran mutanen biyu

A yanzu haka ana rike mutanen uku a babban ofishin Yansandan SARS dake garin Kaduna, kamar yadda lauyan wadanda aka kama, Sani Katu ya bayyanawa manema labaru, inda ya tabbatar da cewa tsohon mijin Naseeba ne ya sanya aka kamasu.

Sai dai ko da majiyarmu ta tuntubi kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo domin jin ta bakinsa, ya ce ba shi da masaniya game da faruwar lamarin, amma zai yi karin bayani da zarar ya tabbatar.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan