Za Mu Mayar Da Kasafin Kuɗin 2020 Doka Ranar 28 Ga Nuwamba- Majalisar Dattijai

255

Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmad Lawan, ya sake nanata shirin Majalisar Dattijai na amincewa da Kasafin Kuɗin 2020 ranar 28 ga Nuwamba.

Mista Lawan, wanda ya ce kwamitocin Majalisar Dattijan na nan na aiki tuƙuru don ganin sun gama aiki a kan lokaci, ya ce ana sa ran Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Dattijan zai gabatar da rahotonsa ranar 26 ga watan Nuwamba.

Ya ce ya yi imanin cewa Majalisar Wakilai ma tana nan tana aiki tuƙuru don gabatar tare da amincewa da rahoton a ranar 26 ga watan na Nuwamba.

“Mista Lawan ya ce: “Dukkan kwamitocin sun yi ayyukansu yadda ya dace a cikin ƙa’idojin da aka sa musu, kuma ana sa ran Kwamitin Kasafin Kuɗi zai hanzarta ya kawo rahoton a nan zauren Majalisar Dattijai ranar 26 ga watan Nuwamba, makonni biyu masu zuwa.

“Na yi imanin cewa hakan ma za ta faru a zauren ‘yar uwarmu, Majalisar Wakilai, don mu iya mayar da kasafin kuɗin 2020 doka ranar 28 ga Nuwamba.

A ranar 8 ga Oktoba, Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kuɗin 2020 da ya kai triliyan N10.33 ga zauren haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Tuni majalisun biyu sun fara aiki game da kasafin kuɗin ta hanyar yin muhawara da kuma miƙa shi ga kwamitocin kasafin kuɗi don yin nazari da gayyatar ma’aikatu, sashe-sashe, hukumomin don kare nasu kasafin kuɗin.

A halin yanzu, kwamitocin Majalisar Dokoki ta Ƙasa kuɗi na ci gaba da gabatar da rahotannisu a gaban Kwamitin Kasafin Kuɗi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan