Buni Ya Bada Kyaututtuka Ga ‘Yan Takarar Da Suka Lashe Gasar Karatun Kur’ani A Yobe

259

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bada kyautar motoci da kujerun aikin Haji ga ‘yan takarar da suka lashe Gasar Karatun Kur’ani da Hukumar Kula da Makarantun Larabci da na Islamiyya ta Jihar ta shirya.

Majiyarmu ta ruwaito cewa waɗanda suka yi nasarar sun tafi gida da kyaututtuka daban-daban.

Gasar ta tattara ‘yan takara daga ƙananan hukumomi 17 na jihar, waɗanda suka yi nasarar za su wakilci jihar a Gasar Karatun Kur’ani ta Ƙasa da za a yi a Legas nan ba da daɗewa ba.

Alaramma Maina Mohammed daga ƙaramar hukumar Machina shi ya yi nasara a ajin Izifi 60 da Tajwidi, a ɓangaren maza.

Malama Halima daga ƙaramar hukumar Damaturu ita ce ta zo ta ɗaya a ɓangaren mata, inda kowanne da ya yi nasara ya tafi gida da sabuwar mota ƙirar Toyota, da kuma kuma kujerar aikin Haji daga gwamnan.

Gwamna Buni, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Idi Gubana, ya shawarci Musulmi da su zuba dukiyarsu wajen ɗaukaka addinin Allah ta hanyar hidimata wa al’umma.

“A matsayin Musulmi na gari, ya kamata mu ci gaba da dangantaka kawunanmu da kyawawan laduban addinin ta hanyar kashe dukiyarmu wajen haɓaka duk wani abu mai kyau kuma wanda zai amfani al’umma kuma a lokaci guda mu riƙa yin hani ga mummuna”, in ji shi.

Gwamnan ya hori waɗanda suka lashe gasar da su ƙara zage dantse a yayinda za su wakilci jihar a Gasar Karatun Kur’ani ta Ƙasa don su samu damar wakiltar ƙasar nan a matakin ƙasa da ƙasa.

“Saboda haka, ƙwazonku zai zaburar da al’ummomi masu zuwa, daga nan kuma mafarkinmu na zama ɗaya daga cikin cibiyoyin Musulunci mafiya martaba zai zama gaskiya.

“Ga ‘yan takarar da ba su samu zuwa matakin ƙasa ba, zan so in yi kira a gare su da su ƙara ƙoƙari a nan gaba”, in ji Mista Gubana.

Babban Sakataren Hukumar Kula da Makarantun Larabci da na Islamiyya, Mohammed Gujba, ya gode wa gwamnan bisa goyon bayansa wanda ya sa aka kammala gasar cikin nasara.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan