Kwakwalwar Mata Ta Fi Ta Maza Aiki Da Kuma Kaifi – Bincike

1788

Wasu kwararrun masana ilimin halayyar Adam na jami’ar Calofornia da ke kasar Amurka sun gano cewa kwakwalwar ‘ya mace ta fi ta namiji aiki da kuma kaifi.


Masanan wadanda suka gudanar da bincike-bincike akan kwakwalwa dubu 46, sun bayyana cewa a fannoni masu dumbin yawa kwakwalwar ‘ya ‘ya mata ta zarce ta maza, in da suka kara da cewa wannan sakamako zai kawo wani sabon numfashi a fagen ilimin kiwon lafiya da kuma hallayar dan adam.

Saboda a yanzu, za’a samun amsoshin tambayoyi masu yawa da masana suka dade suna yi game da cutar Alzheimer.


Tun da farlo dai an wallafa sakamakon wannan binciken ne a mujallar kiwon lafiya ta “Journal of Alzaheimer’s Disease”

Turawa Abokai

1 Sako

  1. Bincike-bincike irin wadannan na kara Mana (mu dalibai) hazaka da kuma kwadayin yin bincike da kanmu. Allah dai ya kara taimakon ku damu baki daya.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan