Majalisar Dattijai Ta Yi Kira Ga Gwamnati Ta Haramta Shigo Da Tufafi Najeriya

216

A ranar Talata ne Majalisar Dattijai ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta haramta shigo da tufafi zuwa ƙasar nan na tsawon shekara biyar don bada damar samar da tufafi a gida.

Wannan ya biyo bayan wani ƙudiri da Sanata Kabir Barkiya ya gabatar a kan “Buƙatar gaggawa wajen farfaɗo da durƙusassun masaƙun ƙasar nan”.

Haka kuma, Majalisar Dattijan ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar da abubuwan da suka wajaba musamman wutar lantarki ga masaƙun cikin gida don farfaɗo da masana’antar.

Ta kuma yi kira ga gwamnatin da ta ƙarfafa gwiwar kamfanonin saƙa tufafi na gida ta hanyar ba su basussuka marasa ruwa da kuma damar samun rancen cikin sauƙi ta hanyar Bankin Masana’antu.

Da yake jawabi a kan ƙudirin, Sanata Barkiya ya ce kamfanonin saƙa tufafi a ƙasar nan sun taka muhimmiyar rawa a ɓangaren kamfanoni na tattalin arziƙin Najeriya inda aka samu kamfanoni fiye da 140 a shekarun 1960 da 1970.

“Kamfanonin saƙa tufafi sun samu bunƙasa da kaso 67%, a 1991 kuma, sun ɗauki kaso 25% na ma’aikata a ɓangaren kamfanoni. A wancan lokaci, kamfanonin saƙa tufafi su ne suka fi ɗaukar ma’aikata banda gwamnati”, in ji shi.

Ya lura da cewa kamfanonin saƙa tufafin sun samu koma baya sosai a shekaru 20 da suka gabata, inda kamfanonin saƙa tufafi da dama kamar Kaduna Textile, Kano Textile, Aba Textile da sauransu suka kulle, suka jefa ma’aikatansu cikin kasuwar neman aiki.

Sanatan ya ce manufofin gwamnati kamar ƙarin haraji, tsadar kayayyakin aiki, da kasuwanci mara iyaka da shigo da tufafi ba ƙaƙƙautawa sun yi mummunan tasiri ga kamfanonin saƙa tufafi na gida.

Sanata Barkiya ya ce farfaɗo da kamfanonin zai samar da ƙarin kuɗin shiga kuma ya taimaka wa gwamnati faɗada tattalin arziƙin ƙasar nan.

A gudunmawarsa, Sanata Robert Boroffice ya ce shigo da tufafi ya faru ne sakamakon durƙushewar masana’antu gida.

“Rufe boda ya zama wani mabuɗi. Caina ta rufe bodarta tsawon shekara 40 saboda masana’antuta da ci gaba.

“Na yi imanin cewa akwai buƙatar a ƙara wa’adin rufe bodar don ba mu damar kintsawa yadda ya kamata”, in ji shi.

Sanata Boroffice ya ce ƙara wa’adin rufe bodar zai zama wata dama da za a iya amfani da ita wajen farfaɗo da kamfanonin saƙa tufafin da sauran masana’antu da shigo da kaya ba bisa ka’ida ba ya yi wa illa.

Sanata Eyinnaya Ababribe, wanda ya saɓa da Sanata Boroffice a kan cewa rufe boda zai farfaɗo da masana’antun saƙa tufafin ya ce: “Rufe boda ba tare da yin wani abu ba zai haifar da wani samun ƙari a wajen samar da tufafi ba”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan