Mata Za Su Fara Ba Motoci Hannu A Saudiyya

217

A Saudiyya mata za su fara bai wa motoci hannu bayan samun horo na musamman kamar yadda jaridar Gazette ta rawaito jaridar Al-Watan ta shaida a ranar Talata.

Matan dai za su hau kan tituna domin bayar da hannu da kula da tsaro da lafiyar masu tafiya a kasa a biranen Riyadh da Qasim da Najran da Tabuk.

Tuni dai aka fara gina musu ofis-ofis a sassa daban-daban na kasar domin fara aiki.

Matan dai za su amfani da kayan aiki da suka hada da kayan sarki da hular kwano da tabarau da dai sauran kayan aiki da aka tanada domin kare mata daga samun rauni.

Wasu daga cikin ayyukan masu bayar da hannun sun hada da tabbatar da cewa kowace mota na da na’urar gargadi da ke da murya da bidiyo da safayar taya da kayan kashe wuta da jakar kayan taimakon gaggawa da kujerun da ba sa cin wuta da kuma na’urorin rufe kofar mota a yanayin gaggawa.
Rahoto daga BBC Hausa

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan