APC Ba Ta Da Ɗan Takara A Zaɓen Gwamnan Bayelsa- Kotu

195

Babbar Kotun Tarayya mai zama a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, ta ce jam’iyyar APC ba ta da ɗan takara a zaɓen gwamnan da za a yi a jihar a ƙarshen mako.

Wannan ci gaba ya zo ne kwanan biyu kafin zaɓe.

Mai Shari’a Jane Inyang shi ne ya jagoranci zaman kotun.

Hukuncin kotun na ranar Alhamis wani ɓangare ne na ƙarar da Heineken Lokpobiri, ɗaya daga cikin masu neman jam’iyyar ta APC ta tsayar da su takara ya shigar.

Mista Lokpobiri, tsohon Ƙaramin Ministan Gona, ya garzaya kotun ne inda yake roƙon da ta bayyana shi a matsayin sahihin ɗan takarar gwamna a APC, ba David Lyon ba.

“Wannan kotu ta yanke hukuncin cewa zaɓen fitar da gwani da jam’iyyar APC a jihar Bayelsa ta yi ba a yi shi bisa doka da tanadin Kundin Tsarin Mulkin jam’iyyar ba”, saboda haka, jam’iyyar ba ta da ɗan takara”, lauyan Mista Lokpobiri, Fitzgerald Olorogun, ya faɗa wa manema labarai haka jim kaɗan bayan yanke hukuncin kotun.

Mista Olorogun ya ce hukuncin kotun ba shi ne addu’arsu ba. “Hukuncin ba a yi zaton sa ba”, in ji shi.

Da aka tambaye shi ko wane mataki wanda yake karewa zai ɗauka a gaba, sai Mista Olorogun ya ce: “Za mu yi abinda ya dace. Amma a halin yanzu, hukuncin kotun shi ne APC ba ta da ɗan takara”.

An jibge ‘yan sanda a ciki da wajen harabar kotun.

‘Yan sanda sun toshe babbar hanyar dake zuwa kotun.

Hatta masu ziyara ma da manema labarai sai da aka caje su kafin a bari su shiga cikin kotun.

Kafin wannan hukunci, Mista Lokpobiri ya yi ta kira ga al’ummar Bayelsa ta su zaɓi APC a zaɓen gwamna da za a yi na 16 ga Nuwamba, duk da ƙarar da ya kai Mista Lyon da jam’iyyar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan