Gajerun Mutane Sun Fi Dogayen Mutane Shiga Damuwa – Bincike

226

Binciken masana ya bayyana cewa, rashin tsayi ko gajarta na sanya wasu irin tunane-tunane a zuciyar mutane. Tun da farko masu binciken sun gano hakan ne akan wasu rukunin mutanen da su ka gudanar binciken akai.

Masu binciken karkashin jagorancin Daniel Freeman, tare da sauran mambobinsa wadanda su ka hada da; Nicole Evans da Rachel Lister da Angus Antley da Mel Slater da kuma Graham Dunn sun gwada binciken na su ne akan wasu mutane. In da su ka bukaci mutanen da su yi tafiya a motar haya,wanda daga baya suka bayyana yanda su ke ji a zuciyarsu.

Masanan sun gano cewa, tsayi na taka rawar gani wajen sakawa mutum kwarin guiwar yin tunani akan cutarwar mutane, kaskanci ko daukaka da sauransu.

Kamar yanda binciken da aka yi a shekarar 2014 ya nuna cewa tsawon mutum kan bashi tunanin tsare kansa sakamakon yunkurin mutane na cutar da shi.

Tun da farko dai mutanen sun kara yin wata tafiyar a motar hayan amma sun zauna ne ta yadda wani yafi wani tsawo amma da gangan. Hakan kuwa ya kawo musu tunani daban-daban a zukatansu, sakamakon banbancin tsayinsu.

Mutanen da tsayinsu ya ragu, sun bayyana cewa, sun ji kaskanci, sun zama koma baya da rashin kwarin guiwa sakamakon rage musu tsayi da aka yi. Duk da kuwa ba a sanar musu cewa an rage musu tsayin ba.

Daya daga cikin fasinjojin ya bayyana yanda ya lura cewa, sauran fasinjojin na masa gatsali duk da kuwa a gaskiyar lamarin ba haka bane.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan