An kiyasta cewa mutum miliyan 422 ne ke fama da ciwon suga, a yayin da ake bukukuwan zagayowar Ranar Ciwon Suga ta Duniya, ga abubuwan da ya kamata ku sani game da wannan ciwon, da yadda za ku iya kiyaye kanku daga kamuwa da shi.
Ciwon suga ko diabetes ciwo ne da kan kasance tare da mai fama da shi na tsawon rayuwa wanda kuma kan yi sanadin mutuwar fiye da mutum miliyan daya a kowace shekara
– kana kowa na iya kamuwa da shi
Ana kamuwa da shi ne a lokacin da jikin dan Adam ya kasa sarrafa dukkan sinadarin suga (gulukos) da ke cikin jini; kuma matsalar kan iya janyo aukuwar bugun zuciya ko shanyewar barin jiki ko makanta ko lalacewar koda har ma a kan yanke kafafuwan mai fama da ciwon.
Kana matsala ce mai kara yaduwa – an kiyasta cewa mutum miliyan 422 na fama da ciwon a fadin duniya – wanda ya nunka masu fama da shi sau hudu idan aka kwatanta da shekaru 30 da suka gabata, kamar yadda alkaluman da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta fitar ke nunawa.
Amma duk da hatsarin da mai fama da ciwon kan shiga, rabin wadanda ke dauke da shi ba su mayar da hankali sosai a kansa ba.
Amma sauya yanayin rayuwa na iya taimakawa a kauce wa kamuwa da ciwon. Ga kuma hanyoyin da za a iya bi.
Me ke janyo ciwon suga?
Idan muka ci abinci, jikinmu na sarrafa wani nau’in abinci mai suna kabohaidret (carbohydrate) zuwa sukari (gulukos). Akwai kuma wani sinadari mai suna insulin da jiki kan samar wanda kan umarci jikin da ya yi amfani da sukarin a matsayin makamashi.
Ciwon suga na samuwa ne a yayin da jiki ya daina samar da insulin ko kuma ba ya aiki yadda ya kamata, lamarin da kan janyo taruwar suga a cikin jininmu.
Ciwon suga iri nawa ne?
Akwai ciwon suga iri daban-daban.
A ciwon suga iri na 1, jikin dan Adam kan daina samar da sinadarin insulin, saboda haka sai suga (wanda aka fi sani da sunan gulukos) ya taru a cikin jini.
Likitoci basu san dalilin da yasa hakan ke faruwa ba, amma suna ganin akwai batun gado ko kamuwa da wasu kwayoyin cuta da kan lalata ‘ya’yan halitta masu samar da sinadarin insulin. Kimanin kashi 10 cikin 100 na masu fama da ciwon suga ne ke da nau’i na 1 na ciwon.
A ciwon suga iri na 2 kuma, jikin dan Adam ne ba ya samar da isasshen sinadarin insulin ko kuma insulin din ba ya aiki yadda ya kamata.
Wannan nau’in na samuwa ne a tsakanin masu shekarun haihuwa da suka gota 40 da tsofaffi, amma matasa ma da basu cika motsawa ba ko suka cika zama wuri daya da wani jinsin mutane kamar ‘yan asalin yankin Kudancin Asiya kan kamu da shi.
Wasu mata masu juna biyu ma na iya samun wani nau’i na ciwon suga da kan auku a lokacin da suke dauke da jariri saboda jikinsu ba ya iya samar da isassshen sinadarin insulin da zai wadaci uwar da jaririnta.
A kan sami wasu mutane kuma da ke da wata matsala da ake kira ‘ pre-diabetes ‘, wato wadanda ke dab da kamuwa da ciwon – saboda karuwar sukari a cikin jininsu.
Alamun kamuwa da ciwon suga
Alamun kamuwa da ciwon suga sun hada da:
Jin kishi sosai
Yin fitsari fiye da kima, musamman cikin dare
Gajiya a yawancin lokuta
Ramewa ba tare da dalili ba
Raguwar karfin ido
Ciwon da ya ki warkewa
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Birtaniya, NHS, ta ce a kan gane alamun nau’in na 1 na ciwon suga tun masu shi na kanana ko suna matasa, kuma yafi wahalar da masu fama da shi.
Wadanda kuma ake ganin suna iya kamuwa da nau’i na 2 na ciwon sune wadanda shekarunsu na haihuwa suka kai 40 zuwa sama (ko shekaru 25 a tsakanin ‘yan asalin yankin Kudancin Asiya); ko masu ‘yan uwa da ke da ciwon; ko suna da kiba sosai; ko ‘yan asalin Kudancin Asiya ne; ko ‘yan China ne; ko ‘yan Afirka ne daga yankin Karibiyan ko bakaken fata ne su.
Ina iya kaucewa kamuwa da ciwon suga?
Ciwon na da dangantaka mai karfi ta wajen gado da yanayin da mutum ya sami kansa, amma mutum na iya rage yawan sugar da ke cikin jinin jikinsa ta hanyar kula da irin abincin da yake ci da yawan yadda yake motsa jikinsa.
A matakin farko, ya kamata mutum ya rage cin abinci mai suga da abin sha mai zaki, kuma ya rage cin farin biredi da taliya. A madadin haka sai ya ci wadanda aka yi da alkama.
Abinci mai amfani ya hada da kayan lambu da ganyayyaki da wake da alkama. Akwai kuma man zaitun da kifi.
Yana da muhimmanci mutum ya daina cin abincin da zarar ya ji ya koshi.
Motsa jiki na taimakawa wajen rage bugun jinin jiki da rage yawan suga a jikin dan Adam.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Birtaniya, NHS, ta bayar da shawarar mutum ya rika motsa jikinsa na kimanin sa’a biyu da rabi a kowane mako, wanda ya hada da tafiya da sauri da kuma hawa bene.
Yana kuma da muhimmanci mutum ya guji shan taba kuma ya rage cin abinci mai maiko.
Mutum nawa ne ke dauke da ciwon suga?
Alakaluman da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta fitar na cewa an samu karuwar masu fama da ciwon suga daga mutum miliyan 108 a shekarar 1980 zuwa mutum miliyan 422 a 2014.

Allah yakiyaye