Liverpool da Real Madrid da PSG harma da Manchester United

235

Kungiyoyin kwallon kafa guda 4 rigis wato Liverpool da Real Madrid da PSG da kuma Manchester United sunyi rubdugu wajen neman wani matashin dan wasa da tauraruwarsa ke haskawa.

Tun abaya dai kungiyoyin kwallon kafan Madrid da Manchester United da kuma Paris Saint Germain ne suke nemansa, amma yanzu kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ma tashiga zawarcin wannan dan wasa.

Wannan dan wasa bawani bane face Jadon Sancho dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Brussia Dortmund kuma dan asalin kasar Ingila.

Wannan shi ake cewa allura acikin ruwa mai rabo ka dauka duba da cewa dukkanin kungiyoyin kwallon kafan da suke nemansa manya ne a duniyar kwallon kafa.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan