Ni Da Ƙarin Aure Haihata-Haihata- Ali Nuhu

362

Fitaccen jarumin finafinan Hausan nan, Ali Nuhu ya ce ba shi da burin ƙara aure.

Mista Nuhu ya bayyana haka ne yayinda yake bada amsa ga jerin tambayar da BBC Hausa ta yi masa a wani sabon shiri mai suna Daga Mai Ita.

Ga wasu daga cikin tambayoyin da BBC Hausar ta yi masa.
BBC Hausa: Ko mata nawa kake da burin yi?
Ali Nuhu: A cikin dariya, ɗaya, Maimuna Ali Nuhu.
BBC Hausa: Wace shawar aka fi ba ka?
Ali Nuhu: Shawarar da aka fi ba ni, a kan abinda ya fi shafar sana’ata, yawanci shi ne shawarwarin da ake ba ni, kuma a kan yi min magana ne a kan dangantakata da mutane.
BBC: Waye na hannun damanka a Kannywood?
Ali Nuhu: Na hannun damana a Kannywood, Hafizu Bello.
BBC Hausa: Amma ba a ganin ku tare?
Ali Nuhu: Hafizu Bello darakta ne, kuma tun muna yarinta, har muka girma tare muke da shi, shi ne kuma mutumin da zan ce a Kannywood ba mu taɓa samun tangarɗa ba tun lokacin da muka san juna kafin ma mu shigo har zuwa yanzu.
BBC Hausa: Akwai wata harka da kake yi banda Kannywood?
Ali Nuhu: A yanzu ga shi nan ina ‘Fashion Design’, sannan kuma akwai ‘Poultry’ da nake yi wato kiwon kaji kenan.
BBC Hausa: ‘Ya’yan nawa kake so?
Ali Nuhu: To a burina dai gaskiya ‘ya’ya huɗu nake so in haifa, amma kuma Allahu A’alam.
BBC Hausa: Yin wasa da bada umarni?
Ali Nuhu: A cikin dariya, ai ‘acting’ na fi son ‘acting’.
BBC Hausa: Me ka fi kewa tattare da Borno?
Ali Nuhu: To abinda na fi kewa tattare da Borno, im, Allah Ya ji ƙan kakata, ita na fi kewa ita nake yawan tunawa saboda lokacin da muke ƙanana in muka je hutu yadda take mana, a in muna garin wannan shi ne abinda ba na mantawa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan