Buhari Ya Dawo

174

Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya bayan da ya shafe makonni biyu bisa wata ziyarar ƙashin kai a Landan.

Shugaba Buhari ya sauka a Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 9:45 na dare.

Da yake yi wa manema labarai jawabi a filin jirgin saman, Shugaba Buhari ya ce ya ƙudiri aniyar ƙara yin aiki tuƙuru ga ‘yan Najeriya tare da yi musu adalci.

Rahotonni sun ce jirgin Shugaba Buhari ya bar Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Stansted dake Landan da misalin ƙarfe 3:27 na yamma.

Shugaba Buhari ya tafi Landan ne daga Saudiya bayan ya kammala halarta wani taron zuba jari karo na uku mai suna Future Investment Initiative, FII, a Riyad, babbann birnin Saudiyya.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan