Garin Neman Gira Olympic Eagles Sun Rasa Ido

329

Kungiyar kwallon kafa ta ‘yan kasa da shekara 23 wato Olympic Eagles sun fice daga gasar cin kofin nahiyar Afrika da ake gudanarwa a kasar Masar.

Najeriya sun fice ne biyo bayan kunnen doki da suka tashi tsakaninsu da kasar Afrika ta Kudu wato babu ci.

Najeriya dai sun tafi kasar Masar ne domin jifan tsuntsu biyu da dutse 1 wato su lashe gasar sannan kuma su samowa kasar tikitin buga gasar motsa jiki daza a yi a kasar Japan, inda dutsen nasu ko tsuntsu 1 bai samu ba.

Yanzu dai ta tabbata cewar anfitar da Najeriya awannan gasa sannan kuma basu sami tikitin buga gasar Olympic ba, wannan shi ake cewa ba tsuntsu babu tarko kokuma ace garin nemam gira an rasa ido.

Kasar Ivory Coast ne suke jan ragamar da maki 6 sai Afrika ta Kudu da maki 4 inda Najeriya ke matsayi na 3 da kai 4 sai Zambia amatsayi na karshe da maki 1.

Kasar Ivory Coast ne dai suka fara sanadiyyar ficewar Najeriya daga gasar haka idan za a iya tunawa awasan bangaren mata ma kssar Ivory Coast ne sanadiyyar hanasu samun tikitin buga gasar Olympic.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan