Legas Za Ta Fara Biyan N35,000 A Matsayin Sabon Mafi Ƙarancin Albashi

255

Gwamnatin jihar Legas da Ƙungiyoyin Ƙwadago sun cimma matsaya akan irin tsare-tsaren da za a bi wajen biyan sabon mafi ƙarancin albashi yayinda gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu ya lashi takobin fara biyan N35,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin da zai fara aiki daga watan Nuwamba.

An cimma wannan matsaya ne bayan jerin tarukan tattaunawa tsakanin Hukumar Sasantawa Tsakanin Ma’aikatan Gwamnati ta Jihar Legas.

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, NLC da takwararta ta ‘Yan Kasuwa, TUC sun halarci waɗannan taruka.

Shugaban Hukumar Sasantawa Tsakanin Ma’aikatan Gwamnati ta Jihar Legas, Kwamared Rasaq Adio Falade ya ce an cimma duk wata matsaya da yarjejeniya da ta zama wajibi a ƙarshen tarukan tattaunawar.

An kuma cimma matsaya kan yadda tsarin ƙarin mafi ƙarancin albashin zai kasance ga sauran ma’aikatan gwamnati dake karɓar sama da mafi ƙarancin albashin.

Mista Falade ya ce an yi gyare-gyare kamar haka: Matakin albashi na 01-06=N35,000, matakin albashi na 07=30%, matakin albashi na 08-10=25, matakin albashi na 12-14=22.5% matakin albashi na 15-17=20%.

Labarai24 ta kawo rahoton yadda Ministan Ƙwadago da Samar da Aikin Yi, Chris Ngige ya yi bayanin yadda Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin.

“Ga waɗanda ke kan matakin albashi na farko, COMESS, mataki na 7, za su samu ƙarin kaso 23 cikin ɗari, matakin albashi na 8 za su samu ƙarin kaso 20 cikin ɗari, matakin albashi na 9 za su samu ƙarin kaso 19 cikin ɗari, matakin albashi na 10 zuwa na 14 za su samu ƙarin kaso 16 cikin ɗari, yayinda masu matakin albashi na 15 zuwa na 17 za su samu ƙarin kaso 14 cikin ɗari.

“Waɗanda suke a tsarin albashi kashi na biyu, CONHES, CONRRISE, CONTISS da sauransu, mataki na 7 za su samu ƙarin kaso 22.2 cikin ɗari, mataki na 8 zuwa na 14 za su samu ƙarin kaso 16 cikin ɗari, mataki na 15 zuwa na 17 za su samu ƙarin kaso 10.5 cikin ɗari”, in ji shi.

Mista Falade ya bayyana cewa za a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin ne a jihar Legas a watan nan na Nuwamba

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan