Mai Zai Faru Bayan Tafiyar Singham da Bhahubali A Kano?

177

Jihar Kano yanzu karanta ya kai tsaiko a fannin tsaro, ta wuce lokacin da za’a turo kowanne jami’i (CP) domin shugabantar rundunar yansanda ta jihar. Ba kawai don kasancewarta mafi yawan jama’a a fadin tarayyar Najeriya ba ko don cigaban da take samu a fannonin rayuwa ba, a’a har da kalubalen tsaron da jihar ke fuskanta da yawa.

A baya dai jihohi irinsu Kaduna da Legas ne ke morar gogaggu kuma kwararrun manyan jami’an yansanda a duk lokacin da aka tashi sauyin wajen aiki, watakila saboda girmansu ko kuma don manyan matsalolin tsaro da suke musu barazana.

Kano a baya-bayan nan ta samu jajirtaccen shugabannin yansanda, musamman Muhammad Wakili (Singham) wanda yayi namijin kokari wajen magance matsalar kwacen wayar hannu (Cell Phones) da ta zama ruwan dare da kuma harkar daba (yan sara-suka), tare da dakile amfani da matasa zauna gari banza yayin zabe musamman a zaben gwamna da akayi na farko a Kano ranar 9 ga watan Maris 2019.

Tsohon Kwamishinan Ƴansandan Kano Muhammad Wakili (Singham)

Kana kuma tsohon kwamishinan yayi namijin kokari don dakile kalaman batanci, kiyayya da kuma na tsana (Hate Speech) da ka iya kawo tashin-tashina. Wannan kokarin da yayi ne ya sanya ake masa lakabi da sunan wani zakakurin dansada da ya fito a wani film din Indiya mai suna Singham.

Bayan tafiyarsa mutanan Kano sun yi kewarsa tare da jimamin ko wanda za’a turo don maye gurbinsa zai iya aikin da Singham yayi?

Allah maji rokon bawansa, sai babban sufeton yansanda na kasa Mohammed Adamu ya turo CP Ahmed Iliyasu ne wanda lokacin da yake shugabantar rundunar yansandan jihar Kano yayi matukar kokari sosai wajen taka burgi ga tsagerun matasan dake kwace wayoyin mutane, kana ya saisaitawa manyan jami’an yansanda sahu musamman masu nawa wurin aiki.

Babban sufeton yansanda na kasa Mohammed Adamu

A lokacinsa, saboda jajircewarsa ne ya bankado badakalar #Kano9 ta satar yaya tare da sauya musu addini kana daga bisani a sayar da su a kudancin Nijeriya kamar bayi. Shi ma mutanen Kano suka saka masa da sunan Bhahubali.

Tsohon Kwamishinan Ƴansandan Kano Ahmed Iliyasu

Karin girman da aka yiwa CP Ahmed Iliyasu zuwa AIG ne ya sanya ya samu sauyin wurin aiki daga jihar Kano zuwa jagoratar shiyyar Legas na rundunar yansanda ta kasa. Hakan ta sanya aka aiko sabon kwamishinan yansanda zuwa jihar Kano ta Dabo Tumbin Giwa.

CP Habu Sani Ahmadu ne sabon kwamishinan da aka turo Kano don maye gurbinsa Ahmed Iliyasu.

Kwamishinan Ƴansandan Kano Habu Sani Ahmadu

Sai dai kuma yanzu ido zai komo kansa don ganin ta ina zai fara. Zai iya irin namijin kokarin da wadanda ya gabace shi suka yi? Yaya zai yi da kalubalen tsaron da har yanzu yake damun jihar ta Kano?

Wasu daga cikin kalubalen tsaron da suke damun jihar Kano a yanzu

  • Matsalar kwacen wayar hannu (mobile phone)

Kwamishinonin yansanda biyun da suka gabata sunyi kokarin ragewa matsalar karfi sosai amma sai dai har yanzu akwai burbushinta, wasu unguwanninma baka isa ka shiga da waya bad a zarar dare yayi.

  • Fyade

Har yanzu jihar Kano na fama da matsalar tsofaffin najadu dake yiwa yara kanana fyade da kuma matasa kangararrun da suke yiwa yan mata har matan aure fyade musamman a sabbin unguwannin da suke da karancin al’umma.

  • Baragurbin yansandayansanda

Wannan yafi faruwa da masu yawon dare, inda wasu daga cikin yansanda ke latsa wadanda suka tare, idan sun ga babu mamora sai su nemi ya basu na goro, idan kuma suka ji laushi sai su tsare mutum daga nan sai kwanan ofishin yansanda watakil su iza keyarsa zuwa gaban alkali da tuhumar laifin yawon ta zubar.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan