Wata Budurwa Ta Shafe Watanni Biyu Tana Sharar Barci

318

Wata budurwa mai suna Sharik Tobar, mai shekara 17 ’yar kasar Kolombiya da aka gano tana fama da ciwon yawan barci, hakan ya sa ana yi mata lakabi da ‘Kyakkyawa mai ciwon barci,’ inda take yin barcin wata biyu a jere.

Sharik Tobar, tana zaune ne a birnin Acacias da ke kasar Kolombiya kuma tana dauke wata cuta ce da ake kira Kleine-Lebin wadda ta fara tun tana da shekara biyu. Rahotanni sun ce an samu masu dauke da irin wannan cuta su 40 a duk duniya, kuma duk masu irin wannan cuta suna kasancewa cikin yawan barci.

Idan Sharik ta fara barci tana yin wata biyu a wannan hali, inda mahaifiyarta mai suna Marleny, ce take ciyar da ita abincin mai ruwa-ruwa lokaci zuwa lokaci don lura da lafiyarta tana cikin barcin.

“Bayan barcin kwana 48 a watan Yunin bara ta rasa kwayar halittar da take ba ta damar tuna abu a kwakwalwarta, hakan ya sa wata rana Sharik ta tambayi mahaifiyarta cewa, ke wace ce? Kamar yadda Marleny Tobar, ta bayyana wa kafar labarai ta Caracol.

A bana a tsakanin watan Janairu da Fabrairu, Sharik ta yi barcin kwana 22, kuma duk awa sai mahaifiyarta ta ciyar da ita da hannunta. Duk abin da ta girka sai ta sake sarrafa shi zuwa ruwa-ruwa yadda za ta iya hadiya tana barci.

Mahaifiyar Sharik ta aje aikinta don ta samu isasshen lokacin kula da ’yarta maimakon mika Sharik ga hukumomin kasar Kolombiya.

Akwai lokacin da Marleny, ta bukaci taimako kasancewar Sharik ta fara zama kurma a shekarar 2017, hakan ya sa Shugaban Karamar Hukumar Acacias ya ba su gudunmawar gida maimakon gidan haya da suke ciki.

Shugaban Karamar Hukumar Orlando Gutierrez, ya bayyana wa manema labarai cewa, yanzu haka suna ci gaba da gina madatsun ruwa a yankin da budurwar take don tanadar wa jama’a wadataccen ruwa.

Marleny Tobar, ta bukaci cibiyar lafiya ta tallafa wa ’yarta Sharik da abinci mai gina jiki musamman lokacin da take cikin barcin saboda kada ta rasa wani bangaren na kwakwalwarta. “Wannan shi ne abin da Sharik, ta fi bukata saboda ba ta iya cin abinci kamar yadda sauran mutane ke yi,” inji ta.

Har zuwa yanzu masu binciken cututtuka sun ce ba a gano maganin wannan cuta ba
Rahoton Aminiya

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan