Yan Sanda Sun Ceto Wani Yaro Dan Shekaru 4 Da Aka Yi Garkuwa Da Shi A Kano

196

Rundunar yan sandan jihar Kano sun yi nasarar ceto wani yaro mai kimanin shekaru 4 Mai suna Abdurrahman Dalha Wanda aka yi garkuwa dashi.

Tun da farko jami’an yan sandan sun cafke Anas Isah dan shekaru 22 da umar Hassan Mai shekaru 40 bisa zargin su da sace yaro tare da neman kudin fansa kimanin naira miliyan 4 kafin su saki yaron.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na fasebuk, ya bayyana cewa yan sandan sun yi nasarar ceto yaron cikin koshin lafiya a kauyen Inusawa da ke Karamar Hukumar Ungogo.

A karshe kakakin rundunar yansandan ya ce suna bincike akan wadanda ake zargin, da zarar kuma an kammala za’a gurfanar da su a gaban shari’a.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan