Za A Gabatar Da Ƙorafi Ga Fashola Bisa Lalacewar Hanyar Kano-Gwarzo-Dayi

256

Sakamakon damuwa bisa mummunan yanayin da hanyar Kano-Gwarzo-Dayi, wadda ta haɗa jihohi ke ciki, al’ummomin yankin sun yanke shawarar tura tawaga ta musamman don tattaunawa da Ministan Ayyuka, Babatunde Fashola don samun tallafin gwamnati.

“Za mu je mu gabatar da ƙorafi bisa mummunan yanayin da hanyar Kano-Gwarzo-Dayi ke ciki, wadda ta zama tarkon mutuwa”, Yunusa Haruna-Kayyu ɗan Majalisar Jiha mai wakiltar Mazaɓar Gwarzo, ya faɗa wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN haka ranar Juma’a a Kano.

Ya ce tawagar za ta ƙunshi Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, Mu’azu Magaji; Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Sanata Jibrin-Maliya da kuma ‘yan Majalisar Wakilai daga yankin.

“Ya zama wajibi mu haɗu da ministan don bayyana masa damuwar al’ummarmu a kan lalacewar hanyar.

“Hanya ce mai muhimmanci sosai wadda ta haɗa Kano da jihohi huɗu da Jamhuriyar Nijar.

“An yi wa ramukan dake kan hanyar gyare-gyare da yawa, amma hatta ramukan da aka gyara bara sun lalace.

“Abinda wannan hayar ke buƙata a yanzu shi ne gyara na gaba ɗaya, ba toshe ramuka ba.

“To, muna son Gwamnatin Tarayya ta duba yiwuwar bada kwangila don gyara hanyar gaba ɗaya”, in ji Mista Haruna-Kayyu.

Kamfanin Dillancin na Ƙasa, NAN, ya ruwaito cewa hanyar Kano-Gwarzo-Dayi babbar hanya ce zuwa jihohin Katsina, Sokoto, Zamfara da Kebbi, da kuma wasu sassan Jamhuriyar Nijar.

An gina hanyar ne a zamanin mulkin gwamnatin soja ta Janar Ibrahim Babangida, kuma tun lokacin ba a yi mata wani babban gyara ba.

Ɗan Majalisar ya ce gyaran hanyar gaba ɗaya zai bunƙasa harkokin tattalin arziƙi da na zamantakewa a jihohin huɗu da ma wasu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan