Kano Pillars Sunyi Rashin Nasara Har Gida Awasan Mako na 3

160

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars tayi rashin nasara har gida afilin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a birnin Kanon Dabo.

Kungiyar kwallon kafan ta Kano Pillars din sunyi rashin nasara ne ahannun kungiyar kwallon kafa ta Lobi Stars na garin Makurdi daci 1 mai ban Haushi.

Wasan dai antafi hutun rabin lokaci kowacce kungiya na nema inda sai bayan andawo daga hutun rabin lokaci ne Lobi ta sauya akalar wasan.

Yanzu dai Pillars maki 1 ne dasu inda zasu buga kwantan wasan mako na 2 da kungiyar kwallon kafa ta Akwa Starlets.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan