Ya Kamata A Daina Zabe A Najeriya – Hon Aliyu Sani Madakin Gini

3997

Tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Dala a zauren majalisar tarayyar kasar nan Honrabul Aliyu Sani Madakin Gini, ya bayyana takaicinsa akan yadda ake gudanar da zabubbuka a kasar nan kuma a karkashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

Aliyu Madaki ya yi wannan tsokacin ne a shafinsa na fasebuk, in da ya bayyana cewa bai kamata a cigaba da yin zabe a kasar nan ba, gwara kawai a dinga nada kantomin riko da za su shugabanci jihohi.

Cikin rubutun da ya yi mai taken “Makomar Siyasa a kasata Najeriya karkashin Shugaba Mai “Gaskiya”janaral Muhammadu Buhari” ya yi sharhi akan zabubbukan da aka gudanar a jihar Kano da kuma wadanda ake a jihohnn Kogi da kuma jihar Bayelsa.


“Abin da na gani a zaben Kano musamman re-run (ko in ce maimaita zabe na gwabna) da abin da ya ke faruwa a yanzu a jihar Kogi, ya sa na tabbatar cewa, a wannan kasata mu zamu dade ba muga damokaradiya ba. Sannan a gaskiya ban taba zaton irin haka zata faru karkashin gwamnatin Shugaba Buhari.


Na ji wasu na cewa mene ne laifin Buhari a wannan abubuwa dake fa ruwa? Amsa a nan ita ce,su je su karanta constitution na kasa musamman section 14(2)b.Ya kamata masu wannan maganar su sani, cewa janaral Buhari ya rantse da cewa zai preserves, protect and depend the constitution.


Magana ta gaskiya ya kamata, a daina zabe a kasar nan, janaral Buhari ya dinga nada kantomin riko (Sole Administers) suna zama gwamnoni, sannan su kuma su nada yan majalisa ba sai an yi zabe ba. Haka a kasa janaral Buhari ya nada yan masalisar dattijai da na tarayya.


Zabe a kasata ya koma yaki. Ka debo yan daba, Ka saye ma’aikatan tsaro da INEC, a lokacin janaral Buhari, shi ka ke bukata kaci zabe ba jama’a ba.


Wannan shine halin da muke cikin yau a kasa ta hannun Shugaba “Mai Gaskiya”.
Allah Ya tsayar da mu akan daidai, Amin”
Aliyu Sani Madakin Gini

Turawa Abokai

6 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan