An Jarrabi Shugaba Buhari Da Miyagun Mutane A Gwamnatinsa – Hon. Kawu Sumaila

357

Tsohon wakili a majalisar kasa kuma tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin majalisar wakilai honrabul Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya bayyana cewa an jarrabi shugaba Muhammadu Buhari da miyagun mutane a gwamnatinsa.


Kawu Sumaila ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke wata hira da gidan talabijin na rahama da ke Kano ya yi da shi.

“Kuskure ne wani ya dubi Yan Najeriya yace musu an samu cikkakiyar nasara da ake nema a tafiyarwa ta gwamnatin Buhari tun daga 2015 zuwa yau saboda wasu dalilai masu yawa”

“An jarrabi Shugaban Kasa Buhari da samun wasu mutanen da suke da banbancin manufa ga neman ciyar da kasa gaba da tabbatar da ingancin rayuwa al’umma dashi”

“Akwai tausayi ga dukkan wanda ya shiga harakar siyasa a Najeriya ba tare da sanin Allah ba; don kuwa duk wanda yayi dogaro da wani don cimma nasara, hakika yayi hasara”

In ji Hon Suleiman Abdulrrahaman Kawu Sumaila a hirarsa da Rahma TV Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan