Home / Siyasa / APC Ta Lashe Zaɓen Gwamna A Bayelsa

APC Ta Lashe Zaɓen Gwamna A Bayelsa

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta bayyana David Lyon, ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamna na ranar 16 ga Nuwamba a matsayin wanda ya yi nasara a jihar Bayelsa.

Da yake sanar da sakamakon zaɓen a ranar Litinin da safe, Baturen Tattara Sakamakon Zaɓen Gwamnan, Farfesa Faraday Orunmwese, ya ce Mista Lyon ya samu jimillar ƙuri’u 352,552, yayinda abokin hamayyar da ke biye masa na jam’iyyar PDP, Duoye Diri, ya samu ƙur’u 143,172.

Mista Orunmuwese ya ce an kaɗa jimillar ƙuri’u 505,884, inda aka lissafa 499,551 a matsayin sahihan ƙuri’u.

Ya ƙara da cewa mutane 922,562 sun yi rijistar zaɓe a jihar, inda 517,883 suka kaɗa ƙuri’a.

Mista Lyon, ya yi nasara da ratar ƙuri’u 180,000 bayan da ya lashe zaɓen a ƙananan hukumomi shida daga cikin takwas na jihar.

APC ta yi nasara a ƙananan hukumomin Brass, Ekeremor, Nembe, Ogbia, Southern Ijaw, da Yenagoa, yayinda Mista Diri ya yi nasara a ƙananan hukumomin Kolokuma/Opokuma da Sagbama.

About Hassan Hamza

Check Also

Ni da Obasanjo mu ka kuɓutar da ɗaliban babbar kwalejin gandun daji ta Afaka – Sheikh Gumi

Fitaccen malami Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana rawar da shi da Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *