Babban Birnin Kasar Indiya Shi Ne Birni Mafi Gurbatar Yanayi A Duniya

255

Masana yanayi da iskar shaka mai kyau sun bayyana babban birnin Indiya watau New Delhi a matsayar birnin da tafi ko wace gurbacciyar iska a duniya.


Haka kuma biranen Indiya biyu da suka hada da Kolkata da Mumbai sun kasance daga cikin birane goma marasa tsabta a duniya, a yayinda suka z ona shioda da na takwas kaman yadda hukumar kula da yanayin iska mai tsabta ta Swiss-based IQ AirVisual ta bayyana a ranar juma’a.

A kwanaki tara jera ga juna daga ranar Lahadi 27 ga watan Oktoban shekarar 2019 yanayin iskar da ake shaka a birnin New Delhi ya kasance mai hatsarin gaske, wanda ka iya cutar da dukkanin al’umman birnin’ inji hukumar IQ Air Visual.


Makarantu ma a birnin New Delhi an rufesu a ranakun Alhamis da Juma’a a yayinda iskar shaka ta kasance mai tsananin hatsarin gaske


Bayan bukin Diwali a ranar 28 ga watan Oktoba yanayin iskar birnin ta kara gurbacewa kamar yadda hukumar lafiya ta sanar da cewa ma’aunin gurbatar iskar kasar ta kai 459 lamarin da ya sanya kaddamar da dokar ta baci na fannin lafiya.


A lokacin da ma’aunin iska ya kai AQIs tsakanin 401 zuwa 500 ana bayyana shi a matsayin muni in ya haura 500 kuma ana bayyana shi a matsayin mafi muni wanda ke bukatar daukar matakai domin magance yanayin.


Kotun kolin kasar dai ta yi korafi akan yadda gwamnatin kasar ta kasa magance matsalar gurbatar yanayi dake addabar kasar ta Indiya baki daya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan