Buni Zai Riƙa Bada Kyautar N100,000 Ga Duk Wanda Ya Dasa Bishiya A Yobe

232

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bada kyautar kuɗi N100,000 ga duk wanda ya karɓi iri daga gwamnatin jihar sannan ya raini irin tsawon shekara ɗaya.

Gwamnan, wanda ya bayyana haka yayin ƙaddamar da shirin dashen bishiyoyi da kuma rabon kyautar kuɗi a Damaturu, ya ce an ɓullo da shirin ne don kare muhalli, a kuma mayar da shi wajen da ɗan ɗan Adam zai ji daɗi rayuwa a kuma tabbatar da dawo da kyan muhalli.

A ta bakinsa, kyautar kuɗin da aka tsara don ƙarfafa wa mutane gwiwa don shiga a dama da su wajen kawo ƙarshen ƙalubalen muhalli a jihar, cika alƙawari ne na nuna jin daɗi ga dukkan waɗanda suka tallafa wa ƙoƙarin gwamnati na kawo ƙarshen gurguzowar hamada.

Gwamna Buni, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Idi Gubana, ya ce: “Kamar yadda wata ƙila za ku iya sani, jihar Yobe tana cikin yankin da yake fama da ƙarancin ruwa da kuma wanda yake samun ruwan sama kaɗan da kuma ƙarancin shuke-shuke, hakan bada kariya ‘yar kaɗan ga muhalli.

“Share gonaki don yin noma, sare bishiyoyi ba bisa ka’ida ba don samun makamashi, samar da gawayi da haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba yana munana yanayin”.

Gwamna Buni ya bayyana cewa matsalolin gurguzowar hamada, ɗibar ƙasa da halin da halin da iyakokin koguna ke ciki sun haifar da rashin samun amfanin gona da yawa da harkokin tattalin arziƙi da zamantakewa.

Ya tabbatar da shirin gwamnatin jihar na ci gaba da ɓullo da manufofi da za su ƙarfafa gwiwa don shuka bishiya, yana mai cewa dasa bishiya waraka ne ga matsalolin muhalli dake fuskantar jihar a halin yanzu.

Gwamnan ya yi kira ga shugabannin ƙananan hukumomi, masu riƙe da sarautun gargajiya, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki da su mayar da dashen bishiya abu mafi muhimmanci.

“Haka kuma ina umartar majalisun ƙananan hukumomi da su shigo da makamantan waɗannan kyaututtuka, kuma su kafa kwamitoci daga tushe da zai haɗa da ɗaukar nayinsu don samun cikakkiyar kulawa wajen hana sare bishiyoyi ba bisa ka’ida ba, su kuma tabbatar da bin dokokin kare muhalli don a samu a yi dai-dai da matakin ƙwarewa a duniya”, in ji Mista Gubana.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan