INEC Ta Ayyana Zaɓen Sanatan Kogi Ta Yamma A Matsayin ‘Inconclusive’

381

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta ayyana zaɓen sanatan Kogi ta Yamma a matsayin wanda bai kamamala ba.

INEC ta ce ta ayyana hakan ne saboda ratar dake tsakanin Smart Adeyemi na jam’iyyar APC da Dino Melaye na jam’iyyar PDP ba ta kai yawan mutanen da suka yi rijistar zaɓe a mazaɓu 53 na yankunan yin rijistar 20 inda aka soke zaɓukan ba.

Mista Adeyemi ya samu ƙuri’u 80,118, yayinda Mista Melaye ya samu ƙuri’u 59,548. Yawan ratar ƙuri’un shi ne 20,570. Adadin masu rijistar zaɓe a yankunan da aka soke zaɓen ya kai 43,127.

Baturen Tattara Sakamakon Zaɓen, Olayinde Lawal, wanda ya ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba, ya ce doka ce ta hana shi bayyana wanda ya lashe zaɓen saboda ratar dake tsakanin ‘yan takarar biyu dake gaba.

Ya ce INEC za ta sanar da sabuwar rana don gudanar da zaɓe zagaye na biyu a tashoshin zaɓe 53 kafin a iya bayyana wanda ya yi nasara.

Tuni dai Mista Melaye ya yi watsi da wannan sakamako.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan