Bello Ya Lashe Zaɓen Gwamna A Kogi

188

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta bayyana gwamna mai ci, Yahaya Bello a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan da aka gudanar a jihar Kogi ranar Asabar da ta gabata.

An dakatar da sanar da sakamakon zaɓen ranar Lahadi da yamma bayan da INEC ta sanar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 19 daga cikin 21 na jihar.

Hukumar ta ce har lokacin tana jiran sakamako ne daga ƙananan hukumomin Lokoja da Abaji.

Ta kuma ce akwai buƙatar a warware matsalar sakamakon zaɓen Dekina.

Amma, tun a sakamakon zaɓen da INEC ta sanar ranar Lahadi, Gwamna Bello na jam’iyyar APC yana dab da yin nasara a kan abokin hamayyarsa na kusa na jam’iyyar PDP, Musa Wada.

Bayan kammala sanar da sakamakon zaɓen a ofishin INEC dake Lokoja a ranar Litinin, Baturen Tattara Sakamakon Zaɓen, Farfesa Ibrahim Umar ya ce Gwamna Bello ya samu jimillar ƙuri’u 406,222, inda ya kayar da abokin hamayyarsa na kusa, Mista Wada, wanda ya samu ƙuri’u 189,794.

“Cewa Yahaya Bello na jam’iyyar APC, sakamakon cika ƙa’idojin doka, da samun ƙuri’u mafi yawa, an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen, kuma ya tabbata zaɓaɓɓe”, a cewar Mista Umar.

Sai dai bayan kammala sanar da sakamakon zaɓen, wakilin PDP ya ƙi ya sa hannu a kan sakamakon da INEC ta bayyana.

A ranar Lahadi jam’iyyar ta nesanta kanta daga sakamakon, inda Mista Wada ya yi zargin cewa akwai rashin bin ƙa’idoji a zaɓen da tsoratar da masu zaɓe da “‘yan ta’addar APC suka yi”, da kuma tashin hankali a dukkan faɗin jihar yayinda ake gudanar da zaɓen.

Ya siffanta sakamakon da INEC ta sanar a matsayin “na ƙarya”.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan