Shugaba Buhari Ya Taya Yahaya Bello Murnar Lashe Zabe A Karo Na Biyu

114

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya yi zarra tare da yin kyakykyawar nasara a zaben gwamna da ya gudana a jihar.


Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a cikin sakon taya murna zuwa ga Bello, wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben.


A karshe shugaban ya yabawa yan jam’iyyar APC akan irin jajircewa da su ka yi tare da tsayawa tsayin daka duk da lamari na rikici da ya faru a lokacin zaben, tare da mika ta’aziyya ga yan uwan wadanda suka rasa ransu a lokacin zaben.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan