Tsohon Gwamnan jihar Kano kuma Sanatan Kano tsakiya a yanzu Malam Ibrahim Shekarau ya ce matukar ana so harkar Ilimi ta gyaru a fadin kasar nan ya zama wajibi gwamnatocin jihohi su dauki gabarar gyara tsarin yadda gwamnati ke daukar malaman makarantu.
Malam Ibrahim Shekarau wanda ya sami wakilcin Ahmad S Aruwa ya bayyana hakan ne lokacin bikin cikar kungiyar tsaffin daliban Kabo Old Girls Association KOGA aji na tamanin da tara shekara talatin da kafuwa.
Ahmad S Aruwa ya kara da cewa akwai bukatar tsaffin kungiyoyin Dalibai su rika kokarin kyautatawa Malaman da suka koyarda dasu domin ta sanadiyyar Malaman ne daliban suka zama wasu.
Alhaji Ahmad S Aruwa ya kuma shawarci sauran tsaffin daliban Makarantu dasuyi koyi da irin kokarin da kungiyar ke yi musamman wajen taimako da sada zumunci.
A Karshen taron an gudanar da makaloli dake nuni da muhimmancin zumunci kamar yadda yake a cikin addinin Musulunci.
Rahoton Freedom Radio, Kano
