Zaɓen Kogi: Wada Zai Garzaya Kotu

216

Ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen gwamn da aka gudanar a jihar Kogi a ƙarshen mako, Musa Wada ya bayyana cewa zai garzaya kotu don neman haƙƙinsa bisa abinda ya kira juyin mulki ga abinda mutane ke so.

Da yake jawabi ga manema labarai ranar Litinin a Abuja, Mista Wada ya ce al’ummar jihar Kogi ma sun yi Allah-wadai da yadda aka gudanar da zaɓen da kuma sakamako.

Mista Wada ya ce suna tare da al’ummar Kogi, za kuma su yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin sun ƙwato haƙkin al’umma.

“Za mu bi wannan ƙara har zuwa ƙarshenta kamar yadda dokokin wannan ƙasa ta tanada”, in ji shi.

Mista Wada ya ce abinda ya faru ranar Asabar, 16 ga Nuwamba, wani yaƙi ne ga ra’ayin al’umma.

Ya ƙara da cewa ‘yan bindigar APC sun kai hare-hare a tashoshin zaɓe kuma sun samu kariya daga jami’an ‘yan sanda sun harbi tare da kashe masu zaɓe.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan