Malamai Sun Gayamin Ni Ne Zan Karbi Mulki A Hannu Buhari – Yariman Bakura

479

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Ahmed Sani Yariman Bakura, ya bayyana niyyar takarar kujerar shugaban kasar nan kuma ya ce wasu malamai ne su ka bayyana masa cewa an yi musu wahayin hakan.

Ciki wata hira da tsohon gwamnan ya yi a gidan rediyon Pride FM, Yarima ya bayyana nasarorin da ya samu a matsayinsa na taohon ma’aikacin gwamnati da kuma fagen siyasa.

Yarima ya bayyana cewa ba zai sa ke neman wata kujera a matakin jiha ba, babban burinsa bai wuce gadar kujerar shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

“Na gama takara a jiha, amma tabbas zan yi takarar shugaban kasa. Tuni wasu manyan yan siyasa da Malamai suna aikin ganin an cimma wannan manufa.”

“Ko a daren jiya daya daga cikin Malaman ya kira kuma ya rantse cewa ya ganni a cikin mafarki na zama shugaban kasa, ina cikin irin motar shugaban kasa.”

“jin hakan ya sanya ni ma sai na fada masa wani labari mai alaka da hakan da wani tsohon abokina da mu ka yi makarantar sakandare, kuma ya kasance tsohon kwamishanan a lokacin gwamnatin Mamuda Shikafi ya fada min.”

Ya fada min cewa “Wani balarabe ya bayyana gabansa a Harami, ya gaishe da shi kuma ya ce daga gani kai dan jihar Zamfara ne.”

“Sai ya tambayesa ‘Ina babanmu Sanata Ahmad Sani Yeriman Bakura? Sai abokin ya fada masa cewa ina
nan lafiya.”

“Sai ya ce masa ya isar da gaisuwarsa gareni sannan ya fada musu cewa idan Allah ya yarda, zan jagoranci Najeriya, sai dai idan na mutu.”

“Sai mutumin ya tafi. Yayin da suke kokarin wucewa, sai matar abokina ta bada shawaran cewa a tambayi shi (Balaraben) sunansa saboda saukin isar da sakon.”

“Abinda ya basu mamaki, mutumin ya bace, sun nemeshi sun rasa.”

“Da abokin nawa ya fadawa daya daga cikin malamansa abinda ya fari, Malamin ya fada masa cewa wahayi ne Allah ya aiko.”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan