Jam’iyyar PDP Tana Shirin Dakatar Da Tsohon Shugaban Kasa Jonathan

197

Ziyarar da Shugabannin jam’iyyar APC su ka kaiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan, a gidansa da ke Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa, karkashin jagorancin shugaban jam’iyyarr APC na kasa Adam Oshiomhole ta bar baya da kura.

Tun da farko jam’iyyar PDP da ta sha kaye a zaben Gwamnan jihar da aka yi ranar asabar ta zargi Jonathan da hada kai wajen faduwar jam’iyyar PDP a jihar.

Bisa wannan dalilin ne jam’iyyar PDP ta ce, akwai yiwuwar a dakatar da tsohon shugaban daga jam’iyyar saboda nasarar da dan takarar APC David Lyon, ya samu a zaben gwamnan jihar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan