A ranar Talata ne Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Ƙasa, NPA, ta ce jiragen ruwa 25 na kan hanyar zuwa Najeriya inda za su kawo man fetur, abinci da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum ta mashigar ruwan Apapa da Tin Can Island.
Wata takardar daga NPA ta nuna cewa ana sa ran isowar jiragen ruwan ne daga 16 ga watan Nuwamba zuwa 31 ga watan Disamba.
Ana sa ran 17 daga cikin jiragen ruwan za su kawo man fetur ne da dangoginsa.
Jirage tara kuma za su kawo jiragen ɗaukar kaya da ababen hawa, fayif-fayif na ƙarfe, sikari da kwantenoni ɗauke da kayayyaki daban-daban.
A cewar NPA, jiragen ruwa 17 suna tashoshin jiragen ruwa inda suke jiran izinin tashi da man fetur, kwantena, kananzir da jiragen ɗaukar kaya.
Wasu jiragen ruwan kuma guda 18 suna can suna saukekwantenonin ƙarfe da sikari.