Ma’aikatan Kogi Ba Sa Bi Na Ko Sisi- Bello

244

A ranar Talata ne zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi watsi da iƙirarin cewa ma’aikatan jihar suna bin sa bashin albashi, yana mai jaddada cewa waɗannan zantuka “ƙarairayi ne”, a cewar jaridar Daily Post.

Gwamna Bello ya ce gwamnatisa ta samu cewa ma’aikata a jihar suna bin bashin albashi, ya jaddada cewa shi ma’aikata ba sa bin sa ko sisi.

Zaɓaɓɓen gwamnan, wanda ya bayyana haka a Channels Television, ya kuma yi zargin cewa ‘yan dabar jam’iyyar PDP sun kashe wani mazaunin wata unguwa bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna na ranar Asabar da ta gabata.

Gwamna ya kuma yi zargin cewa an harbi matar mataimakinsa bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Ya ce: “Duk waɗannan rahotonnin dake cewa ana bi na bashin albashi ƙarairayi ne. Ana bin gwamnonin jihar Kogi da suka gabata albashi tun daga Audu zuwa wanda na gada. Ba a bin jihar Kogi ko sisi a matakin jiha, abinda ya rage shi ne 10% na gwamnatin baya.

“Game da durƙusawar da El-Rufa’i ya yi, yana roƙon cewa al’ummar Kogi su yafe wa Bello bisa tabbatar da tsaro da kuma tabbatar da cewa jihar ta zauna lafiya, ba wai don ya kasa biyan albashi ba”.

Game da iƙirarin cewa an kashe mutane a lokacin zaɓen, Gwamna Bello ya ce: “Bayan an bayyana ni a matsayin wanda ya lashe zaɓen, wani ɗan dabar PDP ya kashe wani sannan ya ruga gidan shugabarsu ta mata, amma an kama shi an hukunta shi.

“An harbi matar zaɓaɓɓen mataimakin gwamna, amma mun gode wa Allah ba ta mutu ba, ‘yan sanda suna kan bincike, kuma za su gurfanar da masu laifi a gaba kotu”.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Litinin ne Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta ayyana Gwama Yahaya Bello na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar na ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2019.

Jami’in Tattara Sakamakon Zaɓen na INEC, Farfesa Ibrahim Garba ya bayyana Gwamna Bello a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan da ya samu ƙuri’u 406,222, inda ya doke abokin hamayyarsa mafi kusa, Musa Wada na PDP, wanda ya samu ƙuri’u 189,704.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan